Takin Zamani: Gwamnatin Zulum Ta Dauki Matakin Saukaka Noma a Jihar Borno

Takin Zamani: Gwamnatin Zulum Ta Dauki Matakin Saukaka Noma a Jihar Borno

  • Gwamnatin Borno ta dauki mataki na musamman domin saukaka nona wajen samar da takin zamani ga manoma a fadin jihar
  • Muƙaddashin gwamnan jihar, Umar Usman Kadafur ne ya kaddamar da shirin a dandalin Farm Center da ke birnin Maiduguri
  • Umar Usman Kadafur ya bayyana adadin takin da suka samarwa manoman jihar da kuma yadda za a sayar musu da shi ciki rahusa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Borno: Gwamnatin Borno ta dauki matakin samar da takin zamani domin saukakawa manoma a fadin jihar.

Gwamnatin ta samar da taki ga manoma a farashi mai rahusa yayin da noma ke kankama a wannar shekarar.

Kara karanta wannan

"Duk da masu ja da ikon Allah, mun yiwa mutanen Kano aiki," Gwamna Abba gida gida

Noma a Borno
Gwamnati ta samar da taki ga manoma a Borno. Hoto: Dogo M. Shettima
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa mukaddashin gwamnan jihar, Umar Usman Kadafur ne ya kaddamar da shirin a Maiduguri.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Adadin takin da aka samar a Borno

Mukaddashin gwamnan jihar Borno, Umar Usman Kadafur ya ce sun samar da taki cikin tirela 100 ga manoma.

Usman Kadafur ya kara da cewa an tanadi takin ne domin manoma da ke dukkan kanan hukumomin jihar.

Farashin da za a sayar da takin

Yayin da yake kaddamar da shirin, Umar Usman Kadafur ya ce gwamnati za ta yi sauƙin kashi 50% yayin sayar da takin, rahoton jaridar Blueprint.

Kadafur ya kuma tabbatar da cewa an yi sauƙin ne domin dukkan manona su samu damar sayen takin da kuma inganta noma.

Kadafur: "Ayi amfani da takin da kyau"

Har ila yau, Umar Usman Kadafur ya yi kira ga manoma wajen yin amfani da takin yadda ya kamata domin cin gajiyar sauƙin da gwamna Babagana Zulum ya samar.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Jigawa ta yi albishir ga dalibai masu sha'awar zuwa karatu kasar waje

Ya ce samar da takin na cikin ayyukan alheri da gwamna Zulum ke ƙoƙarin yi domin inganta harkar noma a jihar.

Zulum ya mika mulki ga Kadafur

A wani rahoton, kun ji cewa daga ranar Litinin, 10 ga watan Yuni, jihar Borno ta samu sabon wanda zai jagoranci gudanar da mulkinta na tsawon kwanaki 28.

Gwamna Babagana Umara Zulum ya miƙa ragamar mulkin jihar Borno ga mataimakinsa watau Umar Usman Kadafur yayin da ya tafi kasa mai tsarki domin aikin Hajji.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng