Gwamna Zulum Ya Bayyana Yadda Yake Farin Ciki da Yan Boko Haram/ISWAP Suke Tuba a Borno
- Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umaru Zulum, ya nuna jin dadinsa da yadda yan ta'adda ke tuba su mika makamansu
- Kwamishinan yaɗa labaran jihar Borno, Abba-Jato, shine ya bayyana haka jim kaɗan bayan fitowa daga taron tsaro
- Yace matsin lambar da sojoji ke wa yan ta'addan na ɗaya daga cikin abubuwan da suka jawo wannan nasarar
Borno - Gwamnatin jihar Borno ta bayyana jin daɗinta yayin da ake kara samun karuwar yan ta'adda suna tuba su mika makamansu ga sojoji a jihar, Kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Borno, Alhaji Babakura Abba-Jato, shine ya bayyana haka jim kaɗan bayan kammala taron tsaro a Maiduguri.
Hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) ta ruwaito cewa rundunar sojoji ta sanar da sama da yan ta'adda 100 ne suka mika makamansu cikin mako biyu da suka gabata a jihar Borno.
Rundunar sojin tace mayaƙan na ƙungiyar Boko Haram sun miƙa makamansu tare da iyalansu.
Sojoji sun matsawa yan ta'adda a Borno
Abba-Jato ya bayyana cewa gwamnati na farin ciki da samun wannan cigaban kuma matsin da sojoji suka yi wa yan ta'addan na daga cikin abubuwan da suka taka rawa wajen samun wannan nasarar.
BBC Hausa ta ruwaito kwamishinan na cewa:
"Gwamnati na farin ciki da wannan ci gaba kuma matsin lambar da sojojin ke yi na daya daga cikin abubuwan da suka haifar da nasarar."
"Shirin komar da 'yan gudun hijira muhallansu na asali ya kara samar da wani yanayi na jin cewa zaman lafiya na kara samuwa a Borno."
A wani labarin kuma Akalla Mutum 5 Sun Rasa Rayukansu Yayin da Dakarun Sojoji Suka Fatattaki Yan Bindiga a Kaduna
Gwamnatin Kaduna ta bayyana cewa aƙalla mutum biyar aka kashe a wasu hare-haren da yan bindiga suka kai jihar.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwa shine ya bayyana haka, ymya kara da cewa dakarun sojoji sun dakile yunkurin kai harin.
Asali: Legit.ng