Ranar Dimokuraɗiyya: Shugaba Tinubu Ya Yi Jawabi Kai Tsaye Ga Al’ummar Najeriya
- Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da jawabin kai tsaye ga al'umar Najeriya a ranar Laraba, 12 ga watan Yunin 2024
- Wannan jawabin ya alamta zagayowar ranar dimokuraɗiyyar Najeriya, kuma Shugaba Tinubu ya dauki alkawura da dama a jawabin na sa
- Jawabin shugaban ya fi karkata kan tattalin arziki, sabon mafi ƙarancin albashi, tsaro da dai sauran abubuwan da suka shafi gwamnati
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Rahotanni sun bayyana cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da jawabin kai tsaye ga al'umar Najeriya ta kafofin watsa labarai.
An ce Shugaba Bola Tinubu ya yi jawabin ne domin murnar bikin zagayowar ranar dimokuraɗiyyar Najeriya na wannan shekarar ta 2024.
An ga shugaban kasar na gabatar da jawabin kai tsaye kamar yadda gidan talabijin na Channels ke watsa wa a yanzu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kalli jawabin a kasa:
Gabatar da mafi ƙarancin albashi
A yayin da ya ke jawabin, Shugaba Tinubu ya sanar da cewa gwamnatinsa na dab da kai karshen maganar sabon mafi ƙarancin albashi kamar yadda aka fahimta daga rahoton Vanguard.
Ya ce idan komai ya kammala, zai mika wa majalisar tarayyar kasar domin su amince da shi wanda ya ke da yakinin zai zama mafi dacewa ga ma'aikatan.
A cewar shugaban kasar:
"Ina sane da matsin tattalin arzikin da ake fama da shi a Najeriya. Sama da shekaru ya kamata a gyara tattalin arzikin kasar saboda lalacewa da rashin makoma.
"Tun bayan hawan mu mulki, mun aiwatar da sauye sauye wadanda suka zama tubali ga dorewar tattalin arzikin kasarmu. Nan gaba kowa zai ci moriyar hakan.
"Ko a lokacin da 'yan kwadago suka shiga yajin aiki kan mafi ƙarancin albashi, ba mu takura masu ba, mun kyale su saboda 'yancinsu ne, saboda muna da yakinin yin adalci a gare su."
Alakar dimokuraɗiyya da tattalin arziki
Shugaban kasar ya ce da ace Najeriya na karkashin 'yan mulkin mallaka, to ba makawa 'yan ƙwadago ba za su samu fuskar yin yajin aikin ba.
Ya yi nuni da cewa manufar dimokuraɗiyya a kullum ita ce mutunta 'yancin kowa, amma ba hakan ne zai sa a sauka daga turbad kundin tsarin mulkin kasar ba.
Tinubu ya sha alwashin farfaɗo da tattalin arziki da kuma gabatar da tsare tsare ta yadda za a gina Najeriya ba tare da an kuntatawa wani dan kasar ba.
Kura kurai a sabon taken Najeriya
A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban majalisar dattawan Najeriya, Godswill Akpabio ya gano wasu kura kurai a dangwaye uku a sabon taken Najeriya.
Sanata Godswill Akpabio ya bayyana cewa taken da hukumar wayar da kan jama'a ta kasa (NOA) ta gabatar ba shi ne majalisar tarayya ta amince da shi ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng