Atiku Ya Fadi Babban Mai Laifi Kan Halin Kuncin da Ake Ciki a Najeriya

Atiku Ya Fadi Babban Mai Laifi Kan Halin Kuncin da Ake Ciki a Najeriya

  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya ɗora alhakin halin ƙuncin da ake ciki a ƙasar nan kan jam'iyyar APC mai mulki
  • Ɗan takarar shugaban ƙasan na jam'iyyar PDP a zaɓen 2023 ya yi nuni da cewa jam'iyyar ta jefa ƴan Najeriya cikin talauci da rashin tsaro
  • Atiku ya kuma caccaki jam'iyyun adawa kan gaza dunƙulewa waje ɗaya domin yiwa APC ritaya daga mulkin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya ɗora alhakin halin ƙuncin da ƴan Najeriya suke ciki kan jam’iyyar APC.

Najeriya dai na fuskantar ƙalubalen taɓarɓarewar tattalin arziki, lamarin da ya sanya ƴan ƙasar ke matukar shan wahala wajen biyan buƙatun yau da kullum.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta fusata kan kalaman Atiku da PDP ga Tinubu, ta yi martani mai zafi

Atiku ya caccaki jam'iyyar APC
Atiku ya caccaki APC kan halin kunci a Najeriya Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata domin tunawa da ranar dimokuradiyya, cewar rahoton jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku ya caccaki jam'iyyun adawa a Najeriya

Atiku ya kuma soki jam’iyyun adawa kan kasa haɗa kansu tare da kafa ƙawancen da zai iya wargaza jam’iyyar APC mai mulki, rahoton jaridar Tribune ya tabbatar.

Ya kuma caccaki jam’iyyun adawa saboda kasa gabatar da tsarin shugabanci mai kyau wanda zai samu amincewar ƴan Najeriya.

"A shekara tara da suka gabata an samu wata gwamnati da ta jefa mutanenmu cikin tsabagen talauci da rashin tsaro."
"Abin takaici jam'iyyar APC mai mulki ita ce ke da alhakin jawo wannan halin da ake ciki."
"Amma jam'iyyun adawa suna da na su laifin fiye da na jam'iyya mai mulki saboda yadda suka kasa dunƙulewa waje ɗaya domin samar da shirin yiwa jam'iyya mai mulki ritaya tare da samar da shugabanci mai kyau wanda ƴan Najeriya za su yaba da shi."

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP ta gayawa Tinubu gaskiyar halin da ake ciki a kasa, ta ba shi shawara

- Atiku Abubakar

A cewar tsohon ɗan takarar shugaban ƙasan, babbar barazanar da dimokuraɗiyyar Najeriya ke fuskanta ita ce gazawar jam'iyyun adawa wajen yin adawa yadda ya kamata.

Atiku ya caccaki Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, Atiku Abubakar ya caccaki Tinubu kan yadda yake jan ragamar mulkin Najeriya.

Atiku Abubakar ya bayyana cewa akwai tarin matsaloli da suka dabaibaye tattalin arzikin kasar da Bola Tinubu ya ki bayyanawa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng