Jam'iyyar APC Ta Fusata Kan Kalaman Atiku da PDP ga Tinubu, Ta Yi Martani Mai Zafi

Jam'iyyar APC Ta Fusata Kan Kalaman Atiku da PDP ga Tinubu, Ta Yi Martani Mai Zafi

  • APC mai mulki a Najeriya ba ta ji daɗin kalaman da Atiku Abubakar da jam'iyyarsa ta PDP suka yi ba kan Bola Ahmed Tinubu
  • Jam'iyyar ta bayyana cewa ba daidai ba ne ɗora alhakin halin ƙuncin da ake ciki a ƙasar nan kan Shugaba Tinubu
  • APC ta hannun darektanta na ƙasa ta bayyana cewa akwai laifin Atiku da PDP a halin da ƙasar nan ta tsinci kanta a ciki

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Jam'iyyar APC ta caccaki tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar da jam’iyyarsa ta PDP, bisa ɗora alhakin taɓarɓarewar tattalin arziƙin ƙasa kan Shugaba Bola Tinubu.

Atiku da PDP dai sun ɗora alhakin halin ƙunci da yunwa da ake fama da shi a ƙasar nan kan Tinubu da APC.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya fadi babban abin da tattalin arzikin Najeriya ke bukata

APC ta caccaki Atiku Abubakar
Jam'iyyar APC ta caccaki Atiku da PDP Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Sai dai jam’iyyar APC ta dage kan cewa tsare-tsaren gwamnatin kamar cire tallafin man fetur sun zama wajibi domin ceto ƙasar nan daga durƙushewa baki ɗaya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane martani APC ta yiwa PDP, Atiku?

Da yake mayar da martani a wata tattaunawa ta musamman da jaridar Punch, daraktan jam’iyyar APC na ƙasa, Bala Ibrahim, ya bayyana rashin jin daɗinsa kan kalaman da Atiku da jam’iyyarsa suka yi.

Bala Ibrahim ya bayyana cewa sam babu ƙamshin gaskiya a cikin abubuwan da suka faɗa.

"Tare da girmamawa, ina ganin Atiku bai son faɗin gaskiya. Bai faɗi gaskiya ba kan cewa ba za a iya kwatanta gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da burin Cif MKO Abiola ba. Wannan gwamnati ce ta zo ta aiwatar da burin Abiola."
"Ina ganin Atiku bai son faɗin gaskiya da yake ɗora alhaki kan gwamnatin Tinubu da zarginta da kawo talauci a Najeriya. Siyasa kawai yake yi wanda hakan ba daidai ba ne. Atiku da PDP ya kamata a ɗorawa mafi yawan alhakin."

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP ta gayawa Tinubu gaskiyar halin da ake ciki a kasa, ta ba shi shawara

"Burin PDP saɓanin abin da MKO Abiola ya yi fafutuka a kai ne. Atiku wasan siyasa kawai yake yi kuma yana yin wasan ba daidai ba."

- Bala Ibrahim

Jam'iyyar PDP ta caccaki Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam’iyyar PDP ta zargi jam’iyyar APC da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da jefa ƴan Najeriya cikin tsabagen wahala da talauci.

Jam'iyyar adawan ta bayyana cewa ƴan Najeriya sun fusata kan halin da ƙasar nan ke ciki, inda ta buƙaci Tinubu da ya saurari kiraye-kirayen da ake yi na sauya wasu daga cikin tsare-tsaren gwamnatinsa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng