Kotu Ta Dawo da Basaraken da El Rufai Ya Tuge, Ta Ci Tarar Gwamnatin Kaduna N10m
- Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya tube basarake ana saura kwanaki bakwai ya bar kujerar gwamna
- El-Rufai ya cire Cif Jonathan Pharaguwa daga sarautar Piriga kan zargin sakaci bayan wani rikici ya barke a jihar Kaduna
- Tubabben basaraken ya shigar da kara kotu inda ta yi fatali da korarsa tare da cin gwannatin jihar Kaduna tarar kudi N10m
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kaduna - Kotun masana'antu ta rusa dakatarwar da Nasir El-Rufai ya yi ga wani basarake lokacin mulkinsa a jihar Kaduna.
Kotun ta dauki matakin ne bayan korafin Cif Jonathan Pharaguwa Zamuna da ke sarautar yankin Piriga a karamar hukumar Lere.
Kaduna: Yaushe Nasir El-Rufai ya tube basaraken?
Tsohon gwamnan ya dakatar da basaraken ne a ranar 22 ga wata Mayun 2023 kwanaki kadan kafin mika mulki ga Gwamna Uba Sani, cewar The Guardian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
El-Rufai ya zargi basaraken da sakaci bayan wani rikici a yankin da ya yi sanadin rasa rayuwakan mutane biyu a jihar.
Yayin shari'ar, kotun ta bukaci gwamnatin jihar ta biya basaraken N10m cikin kwanaki 30 saboda asarar da suka jawo masa.
El-Rufai ya tube sarakuna 2 a Kaduna
Idan ba manta ba, Legit Hausa ta kawo muku labarin cewa Nasiru El-Rufai ya tsige rawanin sarakuna har guda biyu a jihar Kaduna.
El-Rufai ya tsige Sarkin Piriga, Mai martaba Jonathan Paragua Zamuna, da kuma basaraken masarautar Arak, mai martaba Aliyu Iliyah Yammah.
Kwamishinar kula da harkokin ƙananan hukumomi a Kaduna, Hajiya Umma Ahmad, ce ta bayyana haka a wata sanarwa da ta fitar a wancan lokaci.
Ta ce Sarakunan biyu za su sauka daga kan karagar mulki kuma wannan mataki ya biyo bayan shawarwarin ma'aikatar kananan hukumomi.
EFCC ta shirya binciken El-Rufai
Kun ji cewa hukumar EFCC ta zabi wasu daga cikin jami'anta domin binciken tsohon gwamnan Kaduna watau Nasir El-Rufai.
Hukumar ta dauki wannan mataki ne domin binciken N423bn da ake zargin El-Rufai lokacin da ya ke mulkin jihar Kaduna.
EFCC ta tabbatar da cewa nan ba da jimawa ba za ta gayyaci tsohon gwamnan domin yi masa tambayoyi kan zargin badakala.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng