Gwamna Radda Ya Samo Mafita Ga Gwamnati Kan Mafi Karancin Albashi

Gwamna Radda Ya Samo Mafita Ga Gwamnati Kan Mafi Karancin Albashi

  • A yayin ake ci gaba da taƙaddama tsakanin ƴan ƙwadago da gwamnatin tarayya kan batun mafi ƙarancin albashi, gwamnan Katsina ya samo mafita
  • Gwamna Dikko Umaru Radda ya yi kiran da a bar kowace jiha a ƙasar nan ta samar da mafi ƙarancin albashin da za ta iya biyan ma'aikatanta
  • Gwamnan ya nuna cewa kuskure ne a samar da mafi ƙarancin albashi na bai ɗaya wanda wasu jihohin ba za su iya aiwatarwa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya bayyana cewa ya kamata a bar kowace gwamnatin jiha ta tsara mafi ƙarancin albashinta.

Gwamna Dikko Radda ya bayyana cewa a Najeriya ne kaɗai ake amfani da tsarin mafi ƙarancin albashi na bai ɗaya.

Kara karanta wannan

Kungiyoyin kwadago sun ba gwamnoni shawara kan mafi karancin albashi

Gwamna Dikko ya yi magana kan mafi karancin albashi
Gwamna Radda ya yi kira da a bar kowace jiha ta samar da mafi karancin albashinta Hoto: @dikko_radda
Asali: Facebook

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin wata tattauna da gidan talabijin na TVC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Taƙaddamar gwamnati da ƴan ƙwadago

A halin yanzu a ƙasar nan, gwamnatin tarayya ce ke da ikon samar da mafi ƙarancin albashin da za a riƙa yin amfani da shi.

Ƙungiyoyin ƙwadago sun buƙaci a ƙarawa ma'aikata albashi biyo bayan cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi.

Yayin da gwamnatin tarayya ta yi tayin N62,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi, ƙungiyoyin ƙwadagon sun dage sai an biya N250,000.

Ra'ayin Radda a kan mafi ƙarancin albashi

Gwamna Dikko Radda ya yi nuni da cewa akwai kuskure a samar da mafi ƙarancin albashi wanda jihohi ba za su iya aiwatar da shi ba.

"A Najeriya ne kawai muke da mafi ƙarancin albashin ma'aikata iri ɗaya a dukkanin jihohi. A wasu ƙasashen, jihohi daban-daban suna da mafi ƙarancin albashin daban-daban bisa yadda za a su iya biya."

Kara karanta wannan

Mafi karancin albashi: Kungiyoyin kwadago sun caccaki gwamnonin Najeriya

"Menene amfanin gwamnatin jiha ta amince za ta biya N100,000 idan ba za ta iya aiwatarwa ba."

- Dikko Umaru Radda

Gwamna Radda ya gwangwaje ma'aikata

A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamna Dikko Umaru Radda na jihar Katsina ya gwangwaje ma’aikata da barka da sallah a faɗin jihar.

Gwamna Radda ya ba da kyautar N15,000 ga duka ma’aikatan jihar yayin da kuma ya ba su bashin N30,000 domin gudanar da bukukuwan salla cikin walwala.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng