Gwamnatin Sokoto Ta Yiwa Malaman Musulunci Kyauta Ana Kukan Tsadar Ragon Layya
- Gwamnan jihar Sokoto, Ahmad Aliyu ya ba malaman addinin Musulunci gwaggwaɓar kyauta domin hidimar sallar layya
- Kwamishinan harkokin addini na jihar Sokoto, Dakta Jabir Sani Mai Hula ne ya bayyana lamarin ga manema labarai
- Dakta Jabir Sani Mai Hula ya kuma bayyana yadda abin ya gudana tare da faɗin kyautar da kowane malamin addini ya samu
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Sokoto - Yayin da aka fara shirye-shiryen sallar layya, gwamantin jihar Sokoto ta ware makudan kudi domin yin hidima ga malaman addinin Musulunci.
Kwamishinan harkokin addinin Musulunci a jihar Sokoto, Dakta Jabir Sani Mai Hula ya bayyana cewa an ware wasu malamai ne aka ba su kyautar.
Sheikh Jabir Sani Mai Hula ya bayyana haka ne a wani sako da ma'aikatar kula da harkokin addini ta jihar Sokoto ta wallafa a shafinta na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kyautar da aka ba malaman Sokoto
Ma'ikatar harkokin addini ta jihar Sokoto ta bayyana cewa an ba kowane malamin addini kyautar N100,000.
Kwamishinan, Dakta Jabir Sani Mai Hula ya tabbatar da cewa an ba malaman kudi a hannu ne kuma an ba su kudin ne domin sayan ragon layya.
Malaman Sokoto nawa suka samu kyautar?
An bayyana cewa an zaɓo malamai ne daga dukkan ƙananan hukumomin jihar Sokoto guda 23.
Kuma a kowace mazaba da ke dukkan ƙananan hukumomin an zabi malamai 10 domin cin gajiyar kyautar.
Dakta Jabir Sani Mai Hula ya tabbatar da cewa shirin ya dauki tsawon kwanaki hudu ana gudanar da shi tun daga Alhamis zuwa jiya Lahadi.
Malamin ya kuma kara da cewa an kammala shirin cikin nasara, adduo'i da fatan alheri ga gwamnatin jihar.
Gwamnati ta rufe hotel a Sokoto
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Sokoto ta tabbatar da rufe Ifoma hotel bayan zarginsu da zama matattarar yada ayyukan barna a fadin jihar.
Har ila yau gwamnatin ta kara da cewa rufe hotel din ya biyo bayan kiraye-kiraye da suka samu daga mutanen garin Sokoto kan bukatar a kulle shi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng