SERAP: An Je Kotu Neman Bayanan Bashin da Buhari, Jonathan da Obasanjo Suka Karbo
- Kungiyar SERAP ta maka gwamnatin tarayya a gaban kotu domin tilastawa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta wallafa bayanan basussukan da tsofaffin gwamnatocin su ka karbo
- Kungiyar na ganin akwai bukatar 'yan Najeriya su san ainihin yadda aka yi da biliyoyin kudaden da aka karbo da sunansu domin su san yadda za su kalli gwamnati
- Daga gwamnatocin da kungiyar ke neman kotu ta tilasta bayyanan bayanan basussukansu akwai tsohuwar gwamnatin Goodluck Jonathan, Umar Musa 'Yar'adua da Olusegun Obasanjo
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Abuja-Kungiyar SERAP da ke bibiyar tattalin arziki da yaki da cin hanci a Najeriya ta shigar da kara gaban kotu ta na kalubalantar rashin bayyana yadda gwamnati ke kashe basussukan da ta karbo da sunan jama'a.
Kungiyar ta shigar da karar ne a Juma’ar da ta gabata inda ta ke rokon kotu ta tilastawa gwamnati ta wallafa dukkanin bayanan basussukan da gwamnatocin baya suka karbo.
Nigerian Tribune ta wallafa cewa daga gwamnatocin da SERAP ke neman bayanan basussukan da su ka karbowa ‘yan Najeriya akwai gwamnatin Olusegun Obasanjo, da Umaru Musa ‘Yar'adua da ta Goodluck Ebele Jonathan da kuma ta Muhammadu Buhari.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"'Yan Najeriya na da hakkin sanin bashi" - SERAP
Kungiyar da ke bibiyar tattalin arziki da yaki da cin hanci a Najeriya (SERAP) ta ce ‘yan Najeriya na da hakkin su san yadda gwamnatocinsu ka kashe biliyoyin basussukan da su ka karba da sunansu.
SERAP na ganin ta haka ne al’umar kasar nan za su san yadda za su kimanta ayyukan kowacce gwamnatin kasar nan, kamar yadda Punch News ta wallafa.
A sanarwar da mataimakin darkatan kungiyar, Kolawole Oluwadare ya fitar, ya ce su na fatan kotun za ta tirsasawa gwamnatin Bola Tinubu fayyacewa jama’a yadda aka kashe kudaden.
Zuwa yanzu kotun ba ta sanya ranar fara sauraren karar da SERAP din ta shigar ba.
SERAP ta maka Sanata Akpabio Kotu
A baya mun kawo mu ku labarin cewa kungiyar SERAP ta maka shugaban majalisa, Sanata Godswill Apkabio gaban kotu ta na neman haramta biyansa kudin fansho.
Lauyoyin ƙungiyar, Kolawole Oluwadare da Ms Valentina Adegoke ne su ka shigar da karar a madadin kungiyar, inda su ke kalubalantar yadda ake biyan wasu sanatoci kudin fansho baya ga albashinsu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng