Karin Albashi: Fitaccen Malamin Addini Ya Fadi Abin Da ’Yan Majalisu Ya Kamata Su Dauka

Karin Albashi: Fitaccen Malamin Addini Ya Fadi Abin Da ’Yan Majalisu Ya Kamata Su Dauka

  • Yayin da ake takun -saka tsakani gwamnati da kungiyar NLC kan mafi karancin albashi, Fasto Ejike Mbaka ya ba da shawara ga gwamnati
  • Mbaka ya ce ya kamata 'yan Majalisun Tarayya da gwamnoni da kuma 'yan Majalisunsu su rika daukar N62,000 a matsayin mafi karancin albashi
  • Wannan na zuwa ne bayan Gwamnatin Tarayya ta sanar da N62,000 a matsayin mafi karancin albashi da za ta iya biya a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Enugu - Fitaccen Fasto a Najeriya, Ejike Mbaka ya yi tsokaci kan mafi karancin albashin a kasar da ake tababa.

Mbaka ya bukaci mayar da mambobin Majalisar Tarayya kan tsarin mafi karancin albashin N62,000 da Gwamnatin Tarayya ta yi tayi.

Kara karanta wannan

NLC, TUC sun aika sabon gargadi ga Tinubu kan mafi karancin albashi

Malamin addini ya ba da shawarar abin da ƴan Majalisu za su dauka a matsayin albashi
Fasto Ejike Mbaka ya koka kan yajin aikin NLC game da karin albashi. Hoto: Nigeria Labour Congress, Adoration Ministry Enugu, Nigeria.
Asali: Facebook

NLC: Fasto ya magantu kan albashin ma'aikata

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Faston ya bayyana haka ne yayin hira da gidan talabijin na AIT bayan bukatar neman karin albashi da kungiyar kwadago ta NLC ta yi.

Ya ce an boye yawan albashin da mambobin Majalisar Tarayya ke dauka wanda ya ke jawo cece-kuce a Najeriya tsakanin al'umma.

Albashi: Shawarar Fasto ga gwamnatin Najeriya

"Akwai alamun an kusa tura 'yan Najeriya bango a kasar nan, wannan shi ne abin da muke tsoro, muna jihar Lagos ranar amma mun gagara dawowa."
"Kamar wasa kungiyar NLC ta shiga filayen jiragen sama inda ta hana duka tashi da saukar jirage, idan haka ya sake faruwa baka san mene zai biyo baya ba."
"Idan an yanke shawarar ba NLC N62,000, meyasa ba za a hada da mambobin Majalisa da gwamnoni da 'yan Majalinsu ba."

Kara karanta wannan

Gwamnan Anambara ya fadi albashin da ya kamata a biya ’yan siyasa a Najeriya

- Ejike Mbaka

Legit Hausa ta tattauna da wani ma'aikacin Gwamnatin Tarayya kan yanayin karin albashi da ake ciki yanzu.

Mustapha Aliyu Biu ya koka kan halin da ma'aikata ke ciki a Najeriya duba da halin kunci.

"A gaskiya ma'aikata a Najeriya suna cikin wani hali amma abin da wannan Faston ya fada ya kamata a duba."
"Idan har ƴan Majalisu suna kwasar kudi babu yadda za su tausayawa talakawa, ko a bangaren ilimi ba su hada ƴaƴansu da namu duka kuma rashin daidaito ne."

- Mustapha Aliyu

Ya ce duk da dai abin da Fasto ya fada zai yi wahala amma ya kamata Tinubu ya duba lamari karin albashi duba da halin da ma'aikata ke ciki a yanzu a Najeriya.

Ma'ikata sun caccaki gwamnoni kan karin albashi

A wani labarin, ma'aikata a Najeriya sun nuna damuwa kan yadda gwamnoni suka ki amincewa da biyan mafi karancin albashi.

Ma'aikatan sun bukaci gwamnonin da su rage yawan albashinsu da alawus domin biyansu hakkikinsu duba da halin da ake ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel