Matakai 10 da Gwamna Abba Ya Dauka Wajen Ayyana Dokar Ta Baci a Kan Ilmi a Kano

Matakai 10 da Gwamna Abba Ya Dauka Wajen Ayyana Dokar Ta Baci a Kan Ilmi a Kano

  • Gwamnatin Kano ta dauki jerin matakan da ake sa rai za su taimaka wajen dawo da kima da martabar ilmin boko
  • Abba Kabir Yusuf ya sanar da cewa an warewa ilmi kusan 30% a kasafin 2024, kuma zai gyara duka makarantu
  • Gwamnan jihar Kano bai tsaya a nan ba, zai kara daukar malamai kuma a kula da wadanda ake da su a yanzu

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - A ranar Asabar, 8 ga watan Yuni 2024, Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta ayyana dokar ta-baci a kan sha’anin ilmi a jihar Kano.

Kamar yadda aka sanar, Mai girma Gwamnan Kano ya dauki wasu jerin matakai da yake ganin za su taimaka wajen bunkasa ilmin zamani.

Kara karanta wannan

Muhimman ayyuka 15 da Gwamnatin Abba tayi cikin shekara 1 a jihar Kano

Abba Kabir Yusuf
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sa dokar ta-baci a kan ilmi a Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Ilmi: Dokar ta baci a jihar Kano

Darekta Janar na yada labaran gidan gwamnatin Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar da jawabi a kan shirin a shafinsa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jawabin Malam Sanusi Bature Dawakin Tofa ya shiga hannun manema labarai a ranar Asabar.

1. Alhaji Abba Kabir yawarewa sha’anin ilmi 29.95% a kasafin kudin shekarar 2024 domin a kula da makarantun sakandaren gwamnati.

2. Daga cikin shiryen shiryen da ake yi akwai gina dakunan bincike 300 a Kano.

3. Abba Kabir Yusuf ya sha alwashin gina dakunan karatu 1000 a zangon karatun boko da za a shiga.

4. Gwamnatin Kano za ta bude duk wasu makarantun gwamnati da aka rufe su a lokacin Abdullahi Ganduje yana mulki a jihar Kano.

5. Har ila yau gwamnatin Kano za ta gyara duka makarantun firamare da kananan sakandare da ake da su a fadin jihar Kano.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta dauki matakan inganta ilimi a Kano

Sauran matakan da gwamnan Kano ya dauka

6. Shigar da kananan yara aji domin ganin an kawo karshen masu gara-ramba, ba su zuwa makarantun zamani.

7. Gwamnati za ta fara ciyar da kowane dalibai sau daya a kowace makarantar firamare.

8. Dawakin Tofa ya ce bayan abinci da za a rika ba dalibai, kowane ‘dan ajin farko a makarantar firamare zai samu kayan makaranta.

9. Malaman nan 5,632 da ke karkashin tsarin BESDA sun samu cikakken aiki da gwamnatin domin a iya horar da ‘yan makaranta da kyau.

10. Za a dauki karin ma’aikata 10, 000 sannan za a dage wajen kara horar da ma’aikatun da ake da su a yau tare da daukar ma'aikata 1, 000 a makarantun gaba da sakandare.

"Gwamna Abba da gaske yake yi" - Hadimi

Hassan Sani Tukur wanda yana cikin masu taimakawa gwamnan Kano a dandalin sada zumunta ya ce matakin zai bunkasa ilmi.

Hassan Sani Tukur ya tabbatarwa Legit a hira cewa Abba da gaske yi wajen aiwatar da wadannan matakai domin farfado da ilmi.

Kara karanta wannan

Kano: Kwankwaso ya fadi abin da ya dauke hankalin Abba a shekara 1 na mulki

Hadimin gwamnan ya ce sun samu abubuwa sun tabarbare bayan shiga ofis.

Gwamnatin Abba ta rusa masarautun Kano

Dama can ana tunanin idan Kwankwasiyya ta karbi mulki, abubuwa za su canza a Kano kuma kun ji labarin yadda aka sauke sarakuna.

Mai ba Abba Kabir Yusuf shawara, Hassan Sani Tukur ya taba cewa idan Allah ya so ranar wata Juma’a Muhammadu Sanusi II zai dawo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel