‘Aikin Banza Ake Yi’ Naziru Sarkin Waka Ya Ragargaji 'Yan Kirifto Masu Jiran Ta Fashe

‘Aikin Banza Ake Yi’ Naziru Sarkin Waka Ya Ragargaji 'Yan Kirifto Masu Jiran Ta Fashe

  • Biyo bayan fashewar Notcoin a watan da ya gabata, matasa maza da mata sun shiga harkar dangwalen Tapswap da sauransu
  • A yayin da matasa ke tsammanin fashewar Tapswap, shahararren mawaki, Naziru Sarkin waka ya musu kalamai masu zafi
  • Naziru Sarkin Waka ya bayyana cewa harkar dangwale ba abu bane mai fa'ida duk da cewa matasa sun shiga harkar ba dare ba rana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - A yayin da hankulan matasa suka karkata zuwa dangwalen Tapswap da sauransu, harkar ta fara samun suka daga shahararrun mutane.

Shahararren mawaki, Naziru M. Ahmad da aka fi sani da Sarkin Waka ya yi kira ga matasa a kan su ajiye harkar sun nemi abin yi na gaskiya.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kai hari a Arewa, sun kashe yan sanda da mutane da asuba

Sarkin waka
Sarkin waka ya ce masu dangwale ba za su ci riba ba. Hoto: SarkinWaka.
Asali: Facebook

Sarkin Waka ya bayyana haka ne a cikin wani bidiyo da Adam Muhammad Mukhtar ya wallafa a shafin Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dangwalen Kirifto zai rage hada-hadar layya

A cikin bidiyon, Naziru Sarkin Waka ya bayyana cewa a halin yanzu matasa da dama sun kashe kudi wajen sayan data da wayoyi masu tsada.

Saboda haka yace za a iya samun karancin hada-hadar sayan raguna a lokacin bikin babbar sallah da za a yi a ranar Lahadi mai zuwa.

Fashewar Kirifton Notcoin yaudara ce

Naziru Sarkin waka ya yi nuni da cewa fashewar Notcoin ce ta saka mutane da dama fadawa harkar dangwale.

Saboda haka ya shawarci masu harkar da su yi kaffa-kaffa kan cewa ana musu shigo-shigo ba zurfi ne domin a kwashe musu kudi.

Dangwale: "Da yaudara ake farawa" - Naziru

Har ila yau, mawakin ya ce yawanci ana yaudarar mutane ne da shiga harkar idan ance musu manyan mutane ma suna yi sai su dauka da gaske ne.

Kara karanta wannan

NLC na neman ƙarin albashi, Tinubu ya bayyana wani muhimmin aiki da zai yi zuwa 2030

Ya ce daga cikin salon da ake yaudarar mutane ana ce musu manyan mutane kamar Aliko Dangote ma suna harkar.

A karshe Sarkin Waka ya yi hannun ka mai sanda inda yace gwargwadon yadda mutum ya dukufa a harkar dangwale gwargwadon yadda zai sha bakar wahala da talauci.

Sarkin Waka ya yi kyauta ga 'yan fim

A wani rahoton, kun ji cewa mawaki Naziru Sarkin Waka ya baiwa dattijuwar jaruma, Ladin Cima kyautar N2m domin ta ja jari.

Haka zalika Naziru ya yiwa Fati Slow wacce ta caccake shi kan furucin da ya yi a baya kyautar N1m domin itama ta ja jarin fara sana'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng