Rarara, Tijjani Gwandu da Taurarin da Suka Yi Nasarar Tallata ‘Yan Takara a Siyasa
Abuja - Bayan dawowar siyasa a shekarar 1998, wakoki sun rika tasiri sosai wajen lashe zabe da samun kujerar mulki a Najeriya.
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Wakoki har a duniyar nan tana jawo hankalin masu yin zabe, ‘yan siyasar Arewacin Najeriya suna amfani da mawaka a yakin zabe.
Legit ta duba, ta zakulo wasu fitattun wakoki da shahararrun mawaka suka rera, wadanda ake ganin sun taimaka wajen lashe zabe.
Fitattun wakokin siyasa a Najeriya
1. 'Wakar Yau Najeriya riko sai mai gaskiya, Baba Buhari kai mu ke so Najeriya'
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shekaru 20 da suka wuce Ibrahim Yala ya rera wakar ‘Yau Najeriya riko sai mai gaskiya, Baba Buhari kai mu ke so Najeriya’.
Wannan waka ta taimaka wajen tallata Muhammadu Buhari a lokacin yana adawa da PDP, duk da a lokacin bai lashe zabe ba.
2. Wakar Dawo dawo
Nazifi Asnanic ya yiwa Rabiu Musa Kwankwaso wakar ‘Dawo dawo’ wanda ta yi tashe a 2011 da PDP ta sake karbe mulkin Kano.
Wakar ta nuna Kanawa sun yi kewar Kwankwaso shekaru takwas bayan Ibrahim Shekarau ya doke shi a karkashin jam’iyyar ANPP.
3. Masu gudu da su gudu
Wakokin da Dauda Kahutu Rarara ya yi a lokacin zaben 2015 sun ba da gudumuwa wajen ganin bayan Goodluck Jonathan da PDP.
Rarara ya yi wakoki irinsu ‘Masu gudu su gudu’ da ‘mai malfa karya ta kure’ a lokacin daga baya mawakin ya juyawa gwarzonsa baya.
4. Abba Gida Gida, Abba
Abba Kabir Yusuf ya kara samun shahara a siyasa ne saboda wakar Abba Gida Gida, Abba wanda Tijjani Gwandu ya rera a 2018.
Wannan waka ta sa farin jinin Abba ya zarce cikin mabiya Kwankwasiyya, ta karkato da akalar ‘yan mata da matan aure a Kano.
5. Ko Gezau! Go gezau!!
A zaben 2023, wata waka da tayi tashe kuma ake ganin ta taimawa APC a Gombe ita ce ‘Ko Gezau’ wanda ‘Dan Musa Gombe ya rera.
Wannan waka ta ba magoya bayan Inuwa Yahaya kwarin gwiwa a lokacin da ya fuskanci barazana daga jam’iyyun PDP da NNPP.
Tarihin dangin Yar'adua a siyasa
Malam Musa Yar’adua shi ne Matawallen Katsina, ku na da labarin cewa ta zuri’arsa mai albarka an samu shugabanni da yawa a yau.
A gidansa aka samu Shehu Musa Yar’adua, Ummaru Musa Yar’adua da Abdulaziz Musa Yar’adua da kuma Murtala Shehu Musa Yar’adua.
Asali: Legit.ng