Abba Gida-Gida ya yi martani a kan hukuncin kotun daukaka kara

Abba Gida-Gida ya yi martani a kan hukuncin kotun daukaka kara

Jam'iyyar PDP da dan takararta a jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, sun nuna rashin gamsuwa da watsi da kararsu da kotun daukaka kara da ke zama a Kaduna tayi a ranar Juma'a.

Karar na kalubalantar hukuncin kotun sauraron kararrakin zabe ne da ta tabbatar da nasarar Abdullahi Umar Ganduje, a matsayin gwamnan jihar Kano a zaben watan Maris na 2019.

Jaridar Solacebase ta ruwaito yadda kotun daukaka karar, wacce ta samu jagorancin Jastis Tijjani Abubakar ta yi watsi da karar jam'iyyar PDP da dan takararta na gwamna a jihar Kano. Kotun ta ce, karar ta kasa bada gamsassun shaidu a kan zargi 24 da take wa Ganduje da APC a jihar Kano.

DUBA WANNAN: Bidiyon CCTV ta nuna ma'aikatan banki suna wawushe kudi kafin 'yan fashi su iso - 'Yan sanda

A takardar da mai magana da yawun Injiniya Abba K. Yusuf ya bada, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya mika ta ga jaridar Solacebase, ta ce, "Kungiyar lauyoyinmu a halin yanzu suna bitar hukuncin. Bayan hakan ne zamu yanke hukuncin abinda yakamata mu yi don kwato 'yancinmu da aka sace a jihar Kano."

"Ba zamu yi kasa a guiwa ba wajen neman adalci wadanda suka fito kwai da kwarkwata don kada kuri'unsu a ranar Asabar, 9 ga watan Maris 2019 ba.Da kuma wadanda aka hantara, aka tsorata ko aka kashe a yayin zaben."

"Muna son amfani da wannan damar don mika godiya ga magoya bayanmu da suka dinga mana addu'a don samun nasara a kotu. Muna tunatar dasu cewa, mu kwantar da hankulanmu don bamu da wata jihar da ta wuce Kano. Zaman lafiya kuwa yafi komai," in ji takardar.

"A matsayinmu na musulmai nagari, mun san mulki a hannun Allah yake kuma yana ba wanda ya so ne, a lokacin da ya so." cewar takardar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel