Kamfanonin 'Yan Kasuwa Sun Fadi Abin da Zai Faru Idan Karin Albashi Ya Kai ₦100,000

Kamfanonin 'Yan Kasuwa Sun Fadi Abin da Zai Faru Idan Karin Albashi Ya Kai ₦100,000

  • Tattaunawa tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyoyin kwadago kan karin mafi ƙarancin albashi yana cigaba da ɗaukan sabon salo
  • Kungiyar ma'aikata masu zaman kansu sun ce ba za su ki amincewa da gwamnatin tarayya ba idan karin albashi ya haura ₦100,000
  • Sai dai kungiyar ta gindaya sharadi ga gwamnatin tarayya idan karin mafi ƙarancin albashi ya haura nauyin aljihun 'ya 'yanta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Kungiyar ma'aikata masu zaman kansu (OPS) ta bayyana matsayar ta kan karin albashi sama da ₦100,000.

Kungiyar ta ce duk da cewa ba za ta iya biyan ma'aikata kudin ba a halin yanzu amma tana da hanyar da za ta samu mafita.

Kara karanta wannan

Alhazan Kano sun samu gata, an fara ciyar da su abinci kyauta a Saudiyya

Karin albashi
Ma’aikata masu zaman kansu sun fadi sharadin karin albashi zuwa ₦100,000. Hoto: Hoto: Pius Utomi Ukpei
Asali: Getty Images

Wani 'dan kungiyar masu ƙananan sana'o'i (NASME) ne bayyana matsayarsu a wata hira da yayi da jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

₦100,000: Matsayar kungiyar OPS kan albashi

Kungiyar ma'aikata masu zaman kansu (OPS) ta ce idan idan karin albashi ya kai ₦100,000 za su dauki matakin neman gwamnati ta cire su a tsarin biyan haraji.

Ya ce idan aka yafe musu haraji ne kawai za su iya biyan kudin, idan hakan bai samu ba kuma dole sai dai a su fita daga cikin alkawarin gwamnati da 'yan kwadago.

Albashin ₦100,000 zai rusa sana'o'i

Kungiyar OPS ta bayyana ƙarara cewa ba za ta iya biyan ma'aikata kudin da ya kai ₦100,000 ba saboda yanayin da tattalin kasar ke ciki.

Ta ce matuƙar za ta biya ₦100,000 to lallai kananan sana'o'i za su rushe saboda ribar za ta tafi a albashin ma'aikata ne gaba daya.

Kara karanta wannan

'Yan ƙwadago na shirin ɗaukar mataki bayan Gwamnatin Tinubu ta miƙa tayin N62,000

Karin albashi: Halin da ake ciki

A halin yanzu dai an samu matsaya tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar OPS a kan ₦62,000 amma kungiyar kwadago na harin ₦250,000

Wanda hakan na nuna cewa har yanzu akwai sauran kallo tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyoyin kwadago.

Karin albashi: Matsayar gwamnonin jihohi

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnonin jihohin Najeriya sun yi taro kan mafi ƙarancin albashi yayin da kwamitin da aka kafa ke ci gaba da tattaunawa da ƴan kwadago.

Wata majiya mai tushe ta bayyana cewa gwamnoni ba za su iya biyan abin da ya haura N70,000 ba bisa la'akari da yanayin tattalin arziki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel