'Yan Kwadago Na Shirin Ɗaukar Mataki Bayan Gwamnatin Tinubu Ta Miƙa Tayin N62,000

'Yan Kwadago Na Shirin Ɗaukar Mataki Bayan Gwamnatin Tinubu Ta Miƙa Tayin N62,000

  • Alamu na nuna abu ne mai wahala ƴan kwadago su amince da N62,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashin ma'aikata
  • Kwamitin da gwamnatin tarayya ta kafa ya ƙarƙare tattaunawa kuma ya faɗi adadin kuɗin da yake ganin za su inganta rayuwar ma'aikata
  • Sai dai har yanzun NLC ba ta ce komai ba duk da ƴan kwadagon sun rage bukatarsu daga N494,000 zuwa N250,000

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Kwamitin da gwamnatin tarayya ta kafa kan sabon mafi ƙarancin albashi ya ƙarƙare zaman tattaunawa a ranar Jumu'a, 7 ga watan Yuni, 2024.

Bayan shafe sa'o'i ana tattake wuri, kwamitin ya bayar da shawarin N62,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashin ma'aikata a Najeriya.

Kara karanta wannan

"Kuɗin sun yi yawa" Gwamnoni sun mayar da martani kan sabon mafi ƙarancin albashi

Shugabannin NLC da TUC.
NLC na iya komawa yajin aiki bayan ta yi watsi da sabon tayin N62,000 Hoto: Nigeria Labour Congress HQ
Asali: Facebook

Jaridar Leaderhship ta tattaro cewa ƴan kwadago sun yi fatali da sabon tayin, inda suka jaddada cewa sun rage bukatarsu zuwa N250,000.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amma gwamnatin tarayya da kamfanoni masu zaman kansu sun amince da N62,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi.

NLC ka iya komawa yajin aiki

Da alamu dai rashin jituwar na iya tilastawa kungiyoyin kwadago NLC da TUC, su sake farfado da yajin aikin da suka sassauta na mako guda.

NLC na duba yuwuwar sake komawa yajin aikin wanda ta ɗage na tsawon kwanaki biyar bayan gwamnati ta tsaya kan sabon tayin.

Idan baku manta ba a baya gwamnatin tarayya ta gabatar da tayin N60,000 wanda ya fusata ƴan kwadago suka fice daga taron.

Suka kuma ayyana shiga yajin aiki kan gazawar gwamnati game da ƙarin albashi da kuma ƙarin kuɗin wutar da aka yiwa ƴan rukunin Band A, The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ministoci 3 da manyan jiga-jigai sun shiga taron kwamitin mafi ƙarancin albashi a Abuja

Bayan haka a ranar Talata, Shugaban kasar ya umarci Ministan Kudi da Tattalin Arziki, Wale Edun, da ya tsara tsarin mafi karancin albashi na kasa cikin sa'o'i 48.

Sai dai har zuwa daren ranar Jumu'a, 7 ga watan Yuni, ana ci gaba da dakon martanin ƙungiyar kwadago a hukumance kan sabon mafi ƙarancin albashin.

Gwamnoni ba zasu iya biyan N60,000 ba

A wani rahoton ƙungiyar gwamnoni 36 na Najeriya (NGF) ta ce mambobinta ba za su iya biyan N60,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi ba.

Mai magana da yawun NGF, Hajiya Halima Salihu ta ce kuɗin sun yi yawa kuma gwamnoni ba za su iya jure biya ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262