Hajjin 2024: Wata Hajiya Daga Najeriya Ta Rasu a Madina

Hajjin 2024: Wata Hajiya Daga Najeriya Ta Rasu a Madina

  • Allah ya yiwa wata Hajiya wacce ta fito daga jihar Neja rasuwa a ƙasa mai tsarki yayin gudanar da aikin Hajjin bana na shekarar 2024
  • Hajiyar mai suna Ramatu Abubakar mai shekara 45 a duniya ta rasu ne a birnin Madina bayan ta kamu da rashin lafiya daga isarsu ƙasa mai tsarki
  • Kakakin hukumar jin daɗin Alhazan jihar Neja wanda ya tabbatar da rasuwarta cikin wata sanarwa ya ce ta rasu ne bayan an garzaya da ita zuwa asibiti domin duba lafiyarta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Kasar Saudiyya - Wata Hajiya daga jihar Neja mai suna Ramatu Abubakar ta riga mu gidan gaskiya a ƙasa mai tsarki.

Hajiyar mai shekara 45 a duniya ta rasu ne a birnin Madinah na ƙasar Saudiyya yayin gudanar da aikin Hajjin bana.

Kara karanta wannan

Basaraken Arewa ya sha da ƙyar a hannun 'yan bindiga, 'yan sanda sun kai masa ɗauki

Hajiya 'yar Najeriya ta rasu a Madina
Wata Hajiya daga jihar Neja ta rasu a Madina Hoto: Inside Haramain
Asali: Twitter

Hajiya ƴar jihar Neja ta rasu a Madina

Hukumar jin daɗin Alhazai ta jihar Neja ta sanar da rasuwar marigayiyar a cikin wata sanarwa, cewar rahoton jaridar Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kakakin hukumar jin daɗin Alhazan ta jihar Neja, Jibrin Usman Kodo, shi ne ya fitar da sanarwar.

A cikin sanarwar ya bayyana cewa marigayiyar na daga cikin Alhazan farko da suka tashi daga tashar jirgin sama ta ƙasa da ƙasa ta Bola Ahmed Tinubu da ke Minna zuwa Saudiyya a satin da ya wuce.

Ya bayyana cewa marigayiyar ta fito ne daga ƙaramar hukumar Bida ta jihar Neja.

Ta rasu ne a birnin Madina bayan ta kamu da rashin lafiya daga isarsu sannan aka garzaya da ita zuwa asibiti inda anan ne ta koma ga mahaliccinta.

Marigayiyar ba ita ba ce ta farko a cikin Alhazan Najeriya da suka riga mu gidan gaskiya a ƙasa mai tsarki yayin gudanar da aikin Hajjin bana na shekarar 2024.

Kara karanta wannan

Majalisar dattawa ta dauki mataki kan mutuwar masu hakar ma'adanai a Neja

Alhaji ɗan Najeriya ya rasu a Makkah

A wani labarin kuma, kun ji cewa ɗaya daga cikin alhazan jihar Legas mai suna, Idris Oloshogbo, ɗan kimanin shekaru 68 a duniya ya rasu a ƙasa mai tsarki.

Likitocin ƙasar Saudiyya ne suka tabbatar da rasuwar Alhaji Oloshogbo a birnin Makkah.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel