"Akwai Doka," Rundunar 'Yan Sanda ta Gargaɗi Direbobin da ke 'Sace' Jami'an Tsaro

"Akwai Doka," Rundunar 'Yan Sanda ta Gargaɗi Direbobin da ke 'Sace' Jami'an Tsaro

  • Rundunar 'yan sandan Najeriya ta bayyana rashin dacewar ɗabi'ar wasu direbobin da ke haɗuwa da jami'an tsaro a titin kasar nan idan an kama su bisa zargin karya doka
  • Jami'in hulda da jama'a na rundunar, ACP Olamuyiwa Adejobi a safiyar Juma'ar nan ya gargaɗi direbobin su tuba daga ɗanyen aiki da su ke yi domin akwai doka
  • Ya ce duk direban da aka kama bisa zargin karya doka, ya bi umarnin jami'an tsaro, sannan ya shigar da ƙorafinsa ta hanyar da ya dace idan an yi masa ba dai-dai ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Abuja- Yadda wasu direbobin kasar nan ke awon gaba da wasu jami'an tsaro idan an tsare su a hanya ya fara ci wa rundunar 'yan sandan kasar nan tuwo a ƙwarya. Akwai faifan bidiyo iri-iri a kafafen sada zumunta da ke nuna yadda wasu direbobi ke tafiya da ɗan sanda ko jami'in ɗamara da ya shigar musu mota idan an tare su a titi.

Kara karanta wannan

Sanusi II vs Aminu Ado: Halin da ake ciki a Kano yayin da kotu ta fara zaman shari'a

Police
Rundunar 'yan sanda ta gargaɗi direbobin da ke awon gaba da jami'an tsaro Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

'Yan sanda sun dawo kan direbobin mota

Lamarin ba ya yiwa rundunar 'yan sanda daɗi, domin da sassafen Juma'ar nan kakakin rundunar na kasa, ACP Olumuyiwa Adejobi, ya ja kunnen direbobin ta shafinsu na X. Ya ce laifi ne babba direba ya 'sace' ɗan sanda ko wani jami'in ɗamara bayan an tare shi ne saboda zargin aikata laifi.

..."Akwai hukunci," 'Yan sanda

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta bayyana cewa guduwa da jami'in tsaro da ke bakin aiki laifi ne da zai dauki tsattsauran hukunci .

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nigerian Tribune ta wallafa cewa kakakin rundunar ACP Olumuyiwa Adejobi ya ce akwai doka da za ta hukunta ma su aikata irin wannan.

Ya shawarci direbobin da aka tare bisa zargin karya doka su bi jami'an cikin ruwan sanyi, sannan su rika miƙa kokensu ga rundunar idan an ɓata musu.

Kara karanta wannan

PDP ta watsawa Atiku ƙasa a ido kan hadaka da Kwankwaso, Obi, ta yi alfahari

'Yan sanda na neman ɓata-gari

A baya mun kawo muku labarin cewa rundunar 'yan sandan Kano ta fara neman wasu iyayen daba guda 13 da ake zargi da rura wutar daba a jihar.

Kwamishinan 'yan sandan jihar CP Muhammad Usaini Gumel ne ya bayyana haka ta cikin sanarwar da kakakin rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel