Ana Tsaka da Shari’ar Sarautar Kano, Abba Ya Biya Wa Ɗalibai 119,903 Kudin NECO
- Gwamnatin jihar Kano ta ware Naira biliyan 2.9 domin biya wa ɗalibai 119,903 kudin jarabawar NECO da NBAIS ta 2024
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya ba da umarnin biyan kudin a wani yunkuri na tabbatar da cewa ƴaƴan talakawa sun yi karatu
- Wasu daga al'umar Kano da Legit Hausa ta zanta da su, sun nuna godiyarsu ga gwamnan jihar kan wannan abin alkairi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya amince a fitar da Naira biliyan 2.9 domin a biya wa ƴaƴan talakawa kuɗin jarabawar NECO da NBAIS.
Akalla ɗalibai 199,903 da suka fito daga gidajen marasa galihu a faɗin jihar Kano ne za su amfana da tallafin kudin a shekarar 2024.
Sharaɗin biyan kuɗin jarabawar NECO a Kano
Kwamishinan ilimi na jihar, Dakta Umar Doguwa ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a yayin ganawa da manema labarai a Kano, in ji jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dakta Umar Doguwa ya ce za a zaɓi daliban da za a ba tallafin ne daga cikin waɗanda suka samu aƙalla makin 'C' a darusa huɗu a jarabawar gwaji ta 'Mock' da aka yi a kwanan baya.
Kwamishinan ilimin ya ce wannan na daga cikin kudurorin gwanatin Abba Yusuf na tabbatar da dalibai marasa galihu sun yi karatu mai zurfi.
Kano: Jajircewar Abba kan karatun ƴaƴan talaka
Rahoton ya nuna cewa gwamnatin jihar za ta biya wa kowane ɗalibi N24,250 kuɗin NECO da kuma N21,000 na kuɗin NBAIS.
Dakta Doguwa ya ce da farko an nemi a biya wa daliban da suka samu 'C' a darusa takwas kaɗai amma Abba ya ƙi yarda.
Kwanishinan ya ce gwamnan jihar ya ba da umarnin a biya kudin jarabawar ga duk ɗalibin da ya samu 'C' a darusa huɗu domin amfanar ƴaƴan talakawa masu yawa.
Jama'ar Kano sun yabawa Abba
A zantawar mu da Abba Hassan, daga karamar hukumar Gezawa ta Kano, ya jinjinawa gwamna jihar, Abba Kabir kan biya wa dalibai kudin jarabawar.
Abba Hassan ya ce tallafin gwamnan ya zo ne dai dai lokacin da al'uma ke fama da abin da za su ci ba wai ta biyan kudin makaranta ko wata jarabawa ba.
Sa'adatu Muhammad, malamar makaranta a Kano ta ce dalibai da dama ba su da halin biyan kudin wannan jarabawar, inda ta bayyana tallafin a matsayin 'ceton ilimin yara'.
Malamar makarantar ta yi kira ga wadanda za su sami tallafin da za su jajurce wajen ganin sun samu sakamako mai kyau a jarabawar domin nuna godiya ga Gwamna Abba Yusuf.
An yi zaman shari'ar masarautar Kano
A wani labarin, mun ruwaito cewa babbar kotun tarayya da ke sauraron shari'ar rigimar masarautar Kano ta yi zama a ranar Alhamis tare da ɗaukar mataki.
A zaman kotun, lauyan gwamnatin jihar, Ibrahim Wangida ya shaida wa Alkali cewa ba su da hurumin sauraron wannan ƙarar, inda ya kafa misalai.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng