Gwamnatin Kano ta ware N489m don biya wa dalibai kudin NECO

Gwamnatin Kano ta ware N489m don biya wa dalibai kudin NECO

- Gwamnatin Jihar Kano ta amince da fitar da Naira miliyan 489.2 don biya wa daliban jihar ta kudin jarrabawar NECO da ta Larabci

- Gwamnatin ta ce daliban da suka yi nasarar samun credit a kalla biyar ciki har da turanci da lissafi a jarrabawar sharen fage ne kawai za su amfana da wannan

- Gwamnatin na jihar Kano ta amince da biya wa daliban jarrabawar ne bayan kwamishinan ilimi na jihar ya gabatar da bukatar ga majalisar zartarwar jihar

Gwamnatin jihar Kano ta amince da fitar da kudi Naira miliyan 489.2 domin biya wa daliban jihar 29,126 kudin jarrabawa kammala sakandare ta NECO da jarabawar Hukumar Shirya Jarabawar Larabci da Addinin Musulunci ta Kasa.

Wannan na cikin wata sanarwa ce da mai magana da yawun maaikatar ilimi ta jihar Kano, Aliyu Yusuf ya fitar a ranar Litinin kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Gwamnatin Kano ta ware N489m don biya wa dalibai kudin NECO
Gwamnatin Kano ta ware N489m don biya wa dalibai kudin NECO
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Imam Mahmoud Dicko: Ɗan siyasar da ya janyo juyin mulki a kasar Mali

A cewar sanarwar, daliban da suka samu a kalla credit biyar ciki har da lissafi da turanci ne a jarrabawar sharen fage kawai za a biya wa kudin jarrabawar.

"Wannan ya biyo bayan bukatun da kwamishinan ilimi na jihar, Sanusi Kiru, ya gabatar wa Majalisar Zartarwa ta jihar," a cewar Sanarwar.

A wani labarin da Legit.ng Hausa ta wallafa Gwamna Ganduje, ya amince da daukar malaman Qur’ani (Alarammomi) 60 a fadin makarantun Almajiranci 15 da ke jihar.

Kwamishinan ilimi na jihar, Sanusi Kiru, a wani jawabi a ranar Talata, ya ce daukar malaman guda 60 a makarantun Almajiranci zai fara aiki ne nan take.

Ya bayyana cewa, “Gwamna Abdullahi Ganduje ne ya amince da hakan biyo bayan wata wasika da hukumar makarantun Islamiyya ta jihar (KSQISMB) ta gabatar a ranar Litinin.

“Daukar wannan aiki ya sake nuna jajircewar gwamnan wajen kawar da bara a titi da kuma rashin ka’ida wajen kafa makarantun Qur’ani ba tare da samar da muhimman gine-gine da suka kamata ba.

“Wadannan gine-gine sun hada da bandaki, dakunan barci da kuma manhajar da zai sa yaran Almajirai haddace Qur’ani da sauran darusa da ake bukata cikin mutunci da tsaro,” in ji shi.

Mista Kiru ya bayyana cewa za a tura malaman guda 60 zuwa sabbin makaratun kwana na Almajiranci da aka samar a kananan hukumomin Bunkure, Madobi da Bagwai.

A cewarsa, sabbin makarantun kari ne ga guda 12 da ake da su a fadin jihar, jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel