Masarautun Kano: Kotu Ta Dauki Mataki Kan Shari'ar da Ake Yi Bayan Zamanta a Yau

Masarautun Kano: Kotu Ta Dauki Mataki Kan Shari'ar da Ake Yi Bayan Zamanta a Yau

  • Yayin da ake ci gaba da sauraran shari'ar masarautun jihar Kano, kotu ta dauki mataki kan korafin da aka shigar
  • Kotun ta dage sauraran karar har zuwa ranar Alhamis 13 ga watan Yuni domin ci gaba daga inda aka tsaya
  • Hakan ya biyo bayan maka Majalisar jihar da kuma Gwamna Abba Kabir a kotu kan rushe masarautun jihar biyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Babbar Kotun Tarayya da ke jihar Kano ta dage sauraron karar da aka shigar kan masarautun jihar.

Kotun ta dage sauraran shari'ar zuwa wani mako a ranar Alhamis 13 ga watan Yuni da muke ciki.

Kotu ta sanya ranar yankin hukunci kan shari'ar masarautun Kano
Kotu ta dage sauraran shari'ar masarautun Kano zuwa wani mako. Hoto: @masarautarkano.
Asali: Twitter

Kano: Kotu ta dage sauraran shari'ar masarautu

Kara karanta wannan

Masarautun Kano: Kotu ta sanya lokacin fara sauraran shari'a, ta fadi ka'idar zama

Wannan na zuwa ne bayan fara sauraran karar a yau Alhamis 6 ga watan Yuni a Kano kan karar da aka shigar, cewar Freedom Radio.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan ya biyo bayan maka Gwamna Abba Kabir da Majalisar jihar tayi a kan matakin rushe masarautu a jihar da Aminu Babba Dan Agundi, cewar Dala FM.

Martanin lauyoyin gwamnati da 'yan majalisar Kano

A zaman kotun, lauyan gwamnati, Barista Mahmud Magaji SAN, ya yi suka kan hurumin kotun inda ya kawo wasu misalai a shari’o’in da Kotun Koli ta yi.

Lauyan Majalisar Dokokin jihar Kano Barista Ibrahim Wangida ya yi suka kan hanyar da mai karar ya bi ya shigar da karar ba ta da tushe.

Wangida ya ce wanda ya shigar da kara ba dan Majalisa ba ne, kuma lokacin da ya shigar da karar an riga an rushe dokar da ta naɗa shi a matsayin Sarkin Dawaki Babba.

Kara karanta wannan

Duk da umarnin kotu da ke neman sauke Sanusi II, Mataimakin Gwamna ya gana da Sarki

Daga bisani ya ce ba shi da hurumin zuwa kotu domin ƙalubalantar abin da Majalisar ta yi.

Sanusi II ya gargadi iyayen kan tarbiyya

A wani labarin, kun ji cewa Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya gargadi iyayen yara wurin tarbiyantar da 'ya'yansu kan tafarki mai kyau.

Sarkin ya ce iyaye suna da muhimmiyar rawa da za su taka wurin tabbatar da tarbiyar 'ya'yansu a cikin al’umma.

Sanusi II ya ja kunnensu da su saka ido kan 'ya'yansu domin tabbatar da kare su daga miyagun kwayoyi da kuma halaye marasa kyau.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel