Najeriya Ta Yi Babban Rashi, Shugabar NCWS Ta Ƙasa Ta Riga Mu Gidan Gaskiya
- Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Allah ya yiwa shugabar ƙungiyar mata NCWS ta ƙasa, Hajiya Lami Adamu Lau rasuwa ranar Talata, 4 ga watan Yuni
- Iyalan marigayyar sun bayyana cewa Hajiya Lami ta je Birnin Kebbi, babban birnin jihar Kebbi domin gudanar da wasu ayyuka lokacin da rashin lafiya ya rufe ta
- Gwamna Agbu Kefas na jihar Taraba ya miƙa sakon ta'aziyya ga iyalai da ƴan uwa a wata sanarwa da mai magana da yawunsa ya fitar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Taraba - Shugabar ƙungiyar mata ta kasa (NCWS), Hajiya Lami Adamu Lau ta riga mu gidan gaskiya.
Ta rasu ne a ranar Talata, 4 ga watan Yuni, a Birnin Kebbi, babban birnin jihar Kebbi, bayan gajeruwar rashin lafiya.
Wasu majiyoyi daga iyalanta a Jalingo, babban birnin jihar Taraba sun tabbatar da rasuwar Hajiya Lami ranar Laraba, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hajiya Lami ta rasu a Kebbi
Sun bayyana cewa marigayyar ta je jihar Kebbi ne domin gudanar da wasu ayyuka, a wannan lokaci ne ta kwanta rashin lafiya har Allah ya yi mata rasuwa.
Marigayiya Lami, ‘yar asalin jihar Taraba, ta rasu ta bar mijinta, Alhaji Adamu Lau, da ƴaƴa da jikoki da dama, rahoton PM News.
Gwamna Kefas ya yi ta'aziyyar Lami
Da yake alhinin wannan babban rashi, Gwamna Agbu Kefas na jihar Taraba ya miƙa sakon ta'aziyya ga iyalai, ƴan uwa da abokan arzikin Hajiya Lami.
Gwamna Kefas ya yi jimamin rasuwar ne a wata sanarwa da ta fito daga hannun babban mai taimaka masa kan harkokin sadarwa, Emmanuel Bello.
Gwamna Kefas ya bayyana marigayiya Lami a matsayin wata albarka daga Taraba da ta shiga kasashen duniya ta bayar da gudummuwa.
Haka nan kuma gwamnan ya yaba da irin gudunmawar da ta bayar a harkokin mata, inda ya ce ta jima ana fafatawa da ita a gwagwarmayar kwato haƙƙin mata.
'Dan sanda DCP Abubakar ya rasu
A wani rahoton kuma, rundunar ƴan sandan Najeriya ta shiga jimami yayin da babban jami'inta ya riga mu gidan gaskiya a ofishinsa a Abuja.
Mataimakin kwamishinan ƴan sanda, DSP Abubakar Muhammad Guri ya rasu jim kaɗan bayan ya shiga ofis a hedkwatar ƴan sanda.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng