Fitaccen Basarake Kuma Tsohon Kwamishinan Ƴan Sanda Ya Kwanta Dama
- An shiga jimami bayan rasuwar basarake a jihar Ekiti wanda kuma ya kasance tsohon kwamishinan ƴan sanda
- Marigayin Alayeluwa Oba Emmanuel Adebayo ya rasu ne a makon da ya wuce inda aka yi jimamin mutuwarsa
- Babban Sifetan ƴan sanda, Kayode Egbetokunya nuna alhini kan rasuwar tsohon ɗan sandan inda ya ce an tafka babban rashi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Ekiti - An tafka babban rashi bayan rasuwar tsohon kwamishina ƴan sanda a Najeriya kuma basarake a jihar Ekiti.
Marigayin, Alayeluwa Oba Emmanuel Adebayo wanda kuma basarake ne a jihar Ekiti ya rasu a makon da ya gabata.
Basarake: Sifietan ƴan sanda ya nuna alhini
Babban Sifetan ƴan sanda a Najeriya, Kayode Egbetokun ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan basaraken.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na kunshe a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi ya fitar a shafin Facebook a yau Laraba 5 ga watan Yuni.
Egbetokun ya nuna alhini inda ya ce tabbas rundunar ta yi babban rashin jajirtacce wanda ya ba da gudunmawa.
"Marigayi Alayeluwa Oba Emmanuel Adebayo ya bar babban gibi ga al'umma kasancewarsa basarake kuma tsohon kwamishinan ɗan sanda a Najeriya."
"Ba za a taba mantawa da jajircewarsa da kwarewa ba da kuma uwa uba gudunmawa da ya bayar ga al'umma."
- Olumuyiwa Adejobi
Tsohon mataimakin kwamishinan ƴan sanda ya rasu
Har ila yau, Egbetokun ya jajantawa iyalan tsohon mataimakin kwamishinan ƴan sanda, DCP Abubakar Guri bayan rasuwarsa.
Ya ce tabbas rundunar ta yi babban rashin haziki kuma jajirtacce wanda ya ba da gudunmawa sosai.
Guri, kafin rasuwarsa ya yi aiki ofishin rundunar da ke Abuja wanda ya rasu a ranar Litinin 3 ga watan Yuni.
Basarake ya riga mu gidan gaskiya
A wani labarin, kun ji cewa an shiga cikin wani irin yanayi bayan rasuwar fitaccen basaraken gargajiya a jihar Osun.
Marigayi Oba Aderemi Adedapo ya rasu ne a yau Asabar 18 ga watan Mayu a asibitin koyarwa na Jami'ar Obafemi Awolowo da ke Ile-Ife.
Kafin rasuwar marigayin, Oba Adedapo shi ke saraurar yankin Ido-Osun da ke karamar hukumar Egbedore a jihar.
Asali: Legit.ng