Zargin Almundahana: Kotu ta yi Umarnin Buga Sammacin Shugaban APC, Ganduje a Jaridu

Zargin Almundahana: Kotu ta yi Umarnin Buga Sammacin Shugaban APC, Ganduje a Jaridu

  • Babbar kotun jiha a Kano ta bayar da umarnin buga sammacin tsohon gwamna, Dr. Abdullahi Umar Ganduje da iyalansa da wasu mutum shida a manyan jaridu biyu
  • Mai shari'a Amina Adamu Aliyu ce ta bayar da umarnin bayan sauraron bukatar lauyoyin gwamnati wanda Zaharaddeen Hamisu Kofar Mata ya gabatar gabanta
  • Ana zargin Dr. Abdullahi Ganduje da sauran mutanen da karkatar da kudin asusun gwamnati $413,000 da karbar makudan kudi da yawansu ya kai N1.38bn na cin hanci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano- Babbar kotun jiha dake zamanta a Kano ta bayar da umarnin a wallafa sammaci ga tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje a manyan jaridun kasar nan biyu.

Kara karanta wannan

"Dalilin da ya sa har yanzu Aminu Ado Bayero yake halastaccen Sarkin Kano"

Ba Abdullahi Ganduje kadai ba, sammancin ya shafi iyalansa da wasu mutane da gwamnatin jihar Kano ke zargi da almundahanar kudin al'uma a mulkinsu.

Abdullahi Ganduje
Kotu ta yi umarnin buga sammacin shugaban APC, Abdullahi Ganduje da iyalansa a manyan jaridu biyu Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

Ana karar Abdullahi Ganduje a kotu

Vanguard News ta wallafa cewa mai shari'a Amina Adamu Aliyu ce ta bayar da umarnin bayan sauraron bukatar lauyan gwamnati.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zaharaddeen Hamisu Kofar Mata ne wanda ya je kotu madadin lauyan da ke jagorantar bangaren gwamnati Ya’u, Adamu Esq a karar.

Ganduje da su wa gwamnati ke kara?

Gwamnatin Abba Kabir Yusuf na karar shugaban jam'iyar APC, kuma tsohon gwamnan Kano har sau biyu, Abdullahi Umar Ganduje, matarsa, Hafsat Abdullahi Ganduje da dansu Umar Abdullahi Umar.

Sauran wadanda ake tuhuma da laifin karkatar da kudin al'umma sun hada da Abubakar Bawuro, Jibrilla Muhammad da kamfanin Safari Textiles Ltd and Lesage General Enterprises, kamar yadda Justice Watch News ta wallafa.

Kara karanta wannan

Wa zai zama Sarkin Kano? Abin da kotuna 2 suka ce game da makomar Sanusi II da Aminu

Mai shari'a Amina Adamu Aliyu ta dage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar 11 Yuli, 2024.

An gurfanar da Ganduje da iyalansa kotu

A baya mun kawo muku rahoton cewa gwamnatin jihar Kano ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar kuma shugaban APC a yanzu, Dr. Abdullahi Umar Ganduje gaban kotu.

Ana zargin Dr. Ganduje da iyalansa da sauran mutum shida da yashe $413,000 daga lalitar gwamnati tare da karbar cin hancin N1.38bn.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel