An Cafke Ɗan Majalisa da Basarake Kan Zargin Daukar Nauyin Ta’addanci a Zamfara
- Rundunar 'yan sandan jihar Zamfara ta ce ta kama wani dan majalisar jiha, hakimi da kuma tsohon shugaban karamar hukuma
- Kwamishinan 'yan sandan jihar, CP Muhammad Dalijan ya ce an kama manyan mutanen ne bisa zarginsu da daukar nauyin ta'addanci a jihar
- CP Muhammad Dalijan ya bayyana hakan ne lokacin da ya karbi bakuncin tawagar Majalisar Dinkin Duniya kan yaƙi da ta'addanci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Gusau, Jihar Zamfara - Rahotanni na nuni da cewa rundunar 'yan sandan jihar Zamfara ta cafke wasu manyan mutane bisa zarginsu da daukar nauyin ta'addanci a jihar.
An kama manyan mutane a Zamfara
Daga cikin wadanda aka kama akwai wani ɗan majalisar jihar, hakimi da kuma tsohon shugaban karamar hukuma.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwamishinan 'yan sandan jihar Zamfara, Muhammad Dalijan ne ya bayyana hakan a hedikwatar rundunar sa ke Gusau, in ji rahoton Channels.
CP Muhammad Dalijan ya bayyana hakan a lokacin da ya karbi bakuncin jami'in da ke kuka da rundunar yaki da ta'addanci, karkashin ofishin majalisar dinkin duniya na UNODC, Thomas Parker.
Sai dai an ce kwamishinan 'yan sandan bai bayyana sunayen manyan mutanen da aka kama bisa daukar nauyin ta'addanci a jihar ba.
An roki MDD ta gina cibiyar gwaje-gwaje
CP Dalijan ya kuma roki Majalisar Ɗinkin Duniya da ta gina cibiyar gwaje-gwaje na binciken ayyukan ta'addanci a Zamfara domin takaita wahalhalun zuwa Legas.
A yayin da Dalijan ya karbi bakuncin Park, ya nemi UN da ta aiwatar da irin ayyukan da ta yi a Maiduguri a nan Zamfara.
Game da matsalar tsaro a Zamfara, kwamishinan ya ba MDD tabbacin ta'addanci ya ragu sosai a jihar saboda kokarin jami'an tsaro na kama 'yan ta'adda da kakkabe wasu.
MDD ta amsa rokon gwamnatin Zamfara
Da ya ke jawabi, Parker ya ce sun je jihar Zamfara ne domin amsa rokon da Gwamna Dauda Lawal ya yi wa majalisar dinkin duniya na ba jihar gudunmawa wajen yaki da matsalar tsaro.
Parker ya shaidawa 'yan sandan cewa suna shirye domin yin nazarin matsalar tsaron jihar da kuma samar da hanyar magance ta gaba daya.
Ofishin UNDOC na Majalisar Dinkin Duniyar ya kaddamar da tattaunawar kwanaki uku da masu ruwa da tsaki a jihar domin magance matsalolin tsaro da suka addabi yankin.
'Yan daba sun kashe soja a Kaduna
A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu 'yan daba da ake kyautata zaton masu kwacen waya ne sun kashe wani sojan Najeriya a jihar Kaduna.
An ce masu kwacen wayar sun kashe sojan mai suna Laftanar I.M Abubakar a Unguwan Sarki da ke cikin birnin jihar a hanyarsa ta komawa gida.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng