Daga karshe Gwamna Matawalle ya bayyana wadanda ke daukar nauyin 'yan ta'adda a Zamfara

Daga karshe Gwamna Matawalle ya bayyana wadanda ke daukar nauyin 'yan ta'adda a Zamfara

- Gwamna Matawalle ya kaddamar da yaki kan masu daukar nauyin ta’addanci a jihar Zamfara

- Matawalle ya kaddamar da hakan ne a ranar Talata, 2 ga watan Maris, a Gusau, babbar birnin jihar

- A cewarsa, wasu yan siyasa da giyar mulki ke diba ne suke daukar nauyin yan bindiga

Bello Mohammed Matawalle, gwamnan jihar Zamfara, ya bayyana cewa wasu yan siyasa da giyar mulki ke diba a jihar wadanda ke zama a Abuja sune silar sace-sacen mutanen da addabi jihar.

PM News ta ruwaito cewa gwamnan ya sha alwashin kama duk wani dan siyasa da ya shiga jihar tare da kudirin amfani da bata gari wajen haddasa fitina.

Legit.ng ta tattaro cewa ya ce babu wani da zai yi ikirarin fin karfin doka a kasar, cewa ya saka kafar wando daya da makiyan zaman lafiya a jihar.

Daga karshe Gwamna Matawalle ya bayyana wadanda ke daukar nauyin 'yan ta'adda a Zamfara
Daga karshe Gwamna Matawalle ya bayyana wadanda ke daukar nauyin 'yan ta'adda a Zamfara Hoto: @Bellomatawalle1
Asali: UGC

KU KARANTA KUMA: Ba yaki ake yi a Najeriya ba, ACF ta bukaci kungiya da ta janye takunkumin abinci kan kudu

Ya bayyana hakan a gidan gwamnati da ke Gusau, babbar birnin jihar, lokacin da tawagar kungiyar gwamnonin Najeriya karkashin jagorancin Gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti suka kai masa ziyara kan sakin daliban makarantar Jangebe a ranar Talata, 2 ga watan Maris.

Matawalle ya yi gargadin cewa babu wanda ya tsarkaka ko ya fi karfin a taba shi, inda ya bayyana cewa shine ke da ragamar kula da harkokin jihar Zamfara, inda ya kalubanci duk wani dan siyasa da ya kiyaye shi ko ya ga aiki da cikawa.

Gwamnan ya bayyana a ranar Lahadi, 28 ga watan Fabrairu, lokacin da tawagar gwamnatin tarayya ta ziyarce shi cewa mutane da dama za su sha mamaki idan ya fallasa wadanda ke daukar nauyin yan bindiga.

Ya bayyana cewa manyan mutane da dama na da hannu a ta’addanci a jihar sannan cewa ba da jimawa ba zunubinsu zai fallasa su.

A wani labarin, Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya mayar da martani ga shawarar da Majalisar Tsaro ta Kasa ta yanke na ayyana jihar ta Zamfara a matsayin haramtaccen yanki ga jirage, Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Ta'addanci: NDLEA ta kwace bindigogi 27 daga hannun wasu mutane a jihar Neja

Mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Manjo-Janar Babagana Monguno (mai ritaya), ne ya bayyana hakan a karshen taron majalisar tsaron kasa da aka yi ranar Talata.

Monguno ya kuma bayyana cewa gwamnatin tarayya ta hana ayyukan hakar ma’adanai a jihar.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Online view pixel