Jami'a Ta Yi Karin Haske Bayan Samun Satifiket Na Digiri a Wurin Mai Tsire
- Hukumar jami'ar jihar Lagos ta yi martani kan samun wani satifiket na digiri a hannun masu siyar da nama a jihar
- Hukumar makarantar ta ce lamarin tsohon labari ne wanda ya faru tun a shekarar 2018 kuma ta riga ta dauki mataki a kai
- Jami'ar ta tabbatar da haka ne a jiya Litinin 3 ga watan Yuni a shafinta na X inda ta shawarci mutane su yi watsi da labarin
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Lagas - Hukumomi a Jami'ar Lagos sun yi martani kan samun satifiket na digiri a wurin mai siyar da suya.
Jami'ar Legas ta ce abin da ya faru ya dade, ba na yanzu ba ne bayan ganin ana zuba suya a cikin takardar satifiket din.
Martanin Jami'ar Lagos kan takardar digiri
Makarantar ta tabbatar da cewa jabun satifiket ne saboda an yi kuskure wurin rubuta sunan mai shi a jiki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Har ila yau, hukumar makarantar ta ce lamarin ya faru ne tun a ranar Laraba 21 ga watan Nuwambar 2018.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hukumar makarantar ta fitar a jiya Litinin 3 ga watan Yuni a shafinta na X.
Jami'ar Lagos ta ce tsohon lamari ne
"Wannan tsohon labari ne, ku yi watsi da shi, lamarin ya faru ne tun a shekarar 2018 kuma Jami'ar ta dauki mataki kan lamarin."
"An lalata satifiket din saboda an yi kuskure wurin rubuta suna a jiki wanda tuni aka gabatar da wani satifiket ga matashin mai suna Abioye."
- LASU
Hukumar makarantar har ila yau, ta ce ya kamata bayan sauya sunan a lalata satifiket din amma an yi kuskure ya fita waje.
An ceto daliban Jami'a 8 a Kogi
A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin jihar Kogi ya sanar da ceto sauran daliban Jami'ar CUSTECH takwas da aka sace.
Ceto daliban ya tabbatar da kubutar da guda 30 kenan a hannun ƴan bindiga bayan maharan sun hallaka biyu daga ciki.
Wannan na zuwa ne bayan miyagu sun farmaki Jami'ar tare da sace daliban a farkon watan Mayu da ta gabata a jihar Kogi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng