Alkalin Alkalan Kano ta Fito da Matsalar da Bangaren Shari'a Yake Fuskanta

Alkalin Alkalan Kano ta Fito da Matsalar da Bangaren Shari'a Yake Fuskanta

  • Babbar mai shari'a ta jihar Kano, Dije Abdu Abdullahi ta ce yadda sauran bangarorin gwamnati ke yin katsalandan a bangaren shari'a na hana aiwatar da gaskiya
  • Ta ce matukar ana bukatar ana samun masu shiga harkokin bangaren, ba za a samu adalci da gaskiyar da ake fatan samu daga lauyoyi da masu shari'a ba
  • Da yake bude taron lauyoyi na shekara-shekara, gwamna Abba Kabir Yusuf ya hori lauyoyi da sauran ma'aikatan bangaren shari'a su tabbatar da adalci da gaskiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kano- Babbar mai shari’a ta Kano, Dije Abdu Aboki ya ta bayyana abin da za a yiwa bangaren shari’a da zai hana yanke hukunci da rashin gaskiya.

Kara karanta wannan

Shugaban majalisa ya fadi muguwar illar da bukatar NLC za ta yiwa ma'aikata

Ta bayyana cewa matukar ana son bangaren ya rika yanke hukuncin gaskiya da gaskiya, dole ne sauran bangarorin gwamnati su daina yi musu katsalandan.

Justice Dije Abdu Aboki
Babbar Mai Shari'a ta Kano Dije Abdu Aboki ta yi takaicin katsalandan din sauran bangarorin gwamnati a shari'a Hoto: High Court of Justice, Kano
Asali: Facebook

Daily Trust ta tattaro cewa babbar jojin ta bayyana haka ne yayin taron lauyoyi na shekara-shekara mai taken 'Tabbatar da adalci a Najeriya: Kalubale da hanyoyin kawo gyara.'

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

‘Akwai kalubale a bangaren shari’a,’ Aboki

Babbar mai shari’a ta jihar Kano, Dije Abdu Aboki ta tabbatar da cewa bangaren shari’a na fuskantar kalubale da dama da ke bukatar kulawar gaggawa.

Ta ce daya daga matsalolin da suka dabaibaye bangaren shi ne rashin tsayawa da kafafunsu, inda ta ce rashin hakan babbar matsala ce.

Mai shari’a Dije ta kara da cewa tabbatar da yancin bangaren shari’a abu ne da zai yiwa kowa dadi a Najeriya, ba wai masu aiki a sashen ba.

Kara karanta wannan

Sarautar Kano: Abin da Sarki Sanusi II ya gargadi hakimai da ciyamomi 44 a kai a fadarsa

Babbar mai shari’a ta Kano ta kuma bayyana yawan shari’un da aka tara a baya, kuma har yanzu ba a saurare su ba da wata matasalar mai zaman kanta.

Gwamnan Kano ya mika bukata ga lauyoyi

Da yake jawabin bude taro, gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf wanda sakataren gwamnati Abdullahi Baffa Bichi ya wakilta, ya bukaci sashen ya yi tsayin daka wajen dabbaka gaskiya.

Ya hore su da tabbatar da kare fatan ‘yan Najeriya na samun adalci a bangaren ba tare da cin amanar jama’a ba.

Sarautar Kano: Kungiyar NBA ta yi magana

A baya mun ruwaito muku cewa kungiyar lauyoyi ta kasa (NBA) ta yi tir da yadda ake wasa da bangaren shari'a a dambarwar masarautar Kano.

Shugaban kungiyar na kasa, Yakubu Maikyau, OON, SAN ya ce lauyoyi da masu shari'a da ke sauraron karar sun yi abin kunya sosai.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.