An Bayyana Abin da Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Tattauna da Nuhu Ribadu

An Bayyana Abin da Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Tattauna da Nuhu Ribadu

  • Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya ziyarci mashawarcin shugaban kasa kan harkokin tsaro, Nuhu Ribado yayin da ake ci gaba da dambarwar masarautar Kano
  • Darakta janar ga gwamna Abba gida-gida kan yada labarai, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya ce shugabannin biyu sun tattauna batutuwan da duka jibanci ci gaban kasa da jiha
  • Wannan na zuwa ne bayan mataimakin gwamnan Kano Aminu AbdulSalam Gwarzo ya zargi Nuhu Ribado da bayar da jiragen da suka shigo da sarki Aminu Ado Bayero Kano

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa

Jihar Kano- Gwamnatin jihar Kano ta bayyana wasu daga abubuwan da gwamna Abba Kabir Yusuf da mashawarcin shugaban kasa kan harkokin tsaro, Nuhu Ribado suka tattauna. A ranar Alhamis ne gwamnan ya kai wa Nuhu Ribado ziyara yayin da ake ci gaba da dambarwar masarautar Kano.

Kara karanta wannan

Sarauta: Bayan Gwamnatin Kano ta nemi afuwa, Abba ya gana da Ribadu a Abuja

Abba Kabir
Gwamna Abba gida-gida ya tattauna zaman lafiya da mashawarcin shugaban kasa kan tsaro Nuhu Ribado Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Asali: Facebook

A sakon da Darakta janar na gwamna Yusuf kan yada labarai, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya wallafa a shafinsa na facebook, ya ce shugabannin sun yi magana kan zama lafiya a kasa baki daya.

Abubuwan da Abba da Ribadu suka tattauna

Sunusi Bature Dawakin Tofa ya bayyana cewa shugabannin biyu sun tattauna batutuwan ci gaban kasa. Haka kuma gwamna Abba Kabir Yusuf ya kuma shaidawa mashawarcin shugaban kasar halin da ake ciki a Kano, kamar yadda Justice watch ta wallafa. Gwamna Abba Gida-gida ya bayyana cewa Kano na zaune lafiya duk da dambarwa masarautar jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sabanin gwamnatin Kano da Ribadu

A baya dai an ji mataimakin gwamnan Kano, Aminu AbdulSalam Gwarzo na zargin Nuhu Ribadu da hannu cikin dawo da Sarkin Kano na 15, Aminu Bayero jihar. Amma daga baya gwamnatin Kano ta janye kalamanta tare da bawa Ribado hakuri.

Kara karanta wannan

Kano: Hakimai na cigaba da yiwa Sanusi II mubaya'a duk da barazanar umarnin Kotu

Sarki Sunusi II ya yi nadin farko a Kano

A baya mun kawo muku labarin yadda sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi II ya yi nadin sarauta na farko tun bayan nada shi da gwamnati ta yi.

Sarkin ya nada Hamisu Mazugal a matsayin mai unguwar Mazugal dake karamar hukumar Dala, inda ya hore shi da yi adalci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel