Kano: “Zaman ’Yan Tauri a Fadar Sarki Sanusi II Ya Jefa Fargaba a Zukatan Jama’a” Dambazau

Kano: “Zaman ’Yan Tauri a Fadar Sarki Sanusi II Ya Jefa Fargaba a Zukatan Jama’a” Dambazau

  • An ruwaito cewa akwai ƙaruwar 'yan tauri a fadar mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II da ke ba da tsaro
  • Sai dai ayyukan wadannan 'yan taurin ya jefa tsoro da fargaba a tsakanin mazauna yankin fadar Sarkin Kano
  • Mutane sun koka kan yadda ayyukan 'yan taurin ke barazana ga rayuwar su da kasuwancin su na yau da kullum

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kano - Mazauna jihar Kano, musamman makwaftan fadar Sarkin Kano, sun koka kan yawaitar 'yan tauri a yankin fadar.

Idan ba a manta ba, mun ruwaito cewa 'yan tauri sun yi wa fadar Sarkin Kano tsinke domin ba da tsaro ga Muhammadu Sanusi II.

Kara karanta wannan

Sarautar Kano: Abin da Sarki Sanusi II ya gargadi hakimai da ciyamomi 44 a kai a fadarsa

Kanawa sun yi magana kan 'yan tauri a fadar sarki
Kano: An fara korafi kan ayyukan 'yan tauri a fadar Sarki Sanusi II. Hoto: @masarautarkano
Asali: Getty Images

Daboon Dambazau, wani ma'abocin shafin X ya bayyana cewa ayyukan 'yan tauri a yankin ya jefa tsoro a zukatan jama'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Mutane sun shiga fargaba" - Dambazau

Dambazau ya ce:

"A cikin kwana bakwai da suka gabata, an samu karuwar adadin 'yan tauri a yankin fadar Sarkin Kano.
"Ayyukan da suke yi ya jefa tsoro da fargaba a tsakanin mazauna yankin, wanda ya shafi rayuwarsu ta yau da kullum."

Daboon Dambazau ya yi kira ga jami'an tsaro da su dauki matakin gaggawa a kan lamarin, yayin da wallafa bidiyon 'yan taurin.

Kalli faifan bidiyo daban daban a kasa:

"Abin da Sanusi II ke da'awa ya faru" - Garba

Shi ma wani ma'abocin shafin na X, Kawu Garba wanda ya wallafa bidoyon 'yan tauri da suka taru a fadar Sarkin Kano ya koka kan cewa:

Kara karanta wannan

An kama mutumin da ake zargin yana kai wa 'yan bindiga makamai a Plateau

"Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya kasance mai da'awar yaki da cusa yaran talakawa a harkar dabanci.
"Sai dai kuma yanzu sarkin ya kasa cewa uffan kan abin da ke faruwa a fada. Wannan abin takaici ne da yaudara, la'akari da matsayarsa a baya."

Mutane sun yi martani kan 'yan tauri

@Olowolagba39300 ya ce:

"Idan 'yan siyasa sun bar kan mulki, suna fadin gaskiya, amma da sun samu mulki sai su shafawa idanunsu toka."

@Princedansadauk ya ce:

"Dama dai 'yayan talakawa ne ke zarginsa a kan hakan, amma ka ga yanzu sai ya kyale su su yi abin da suka fi so. Ina da tabbacin ba shi ya gayyace ba."

Hudubar Sanusi II ta jawo cece-kuce

A wani labarin, mun ruwaito cewa hudubar Sallar Juma'a da Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya gabatar ta jawo cece-kuce kuce.

A yayin da sarkin ya jaddada cewa babu wanda ya isa ya ja da hukuncin Allah, Muaz Magaji, ya soki Sanusi II da cewa ya yi hubar ne domin yin habaici.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel