“Ka Dauki Kaddara”: An Taso Sarkin Kano Sanusi II a Gaba Kan Hudubar Sallar Juma’a

“Ka Dauki Kaddara”: An Taso Sarkin Kano Sanusi II a Gaba Kan Hudubar Sallar Juma’a

  • A ranar Juma'a, 31 ga watan Mayun 2024, Sarkin Kano, Lamido Sanusi ya gabatar a hudubar Sallar Juma'a a masallacin fada
  • Sai dai wannan hudubar da Sanusi II ya gabatar ta dawo cece-kuce yayin da wasu ke zarginsa da amfani da mumbari domin yin habaici
  • Wani ma’abocin Facebook, Adam Muhammed, ya gargadi Sarki Sanusi II kan yin amfani da mumbari wajen tallata manufarsa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kano - Hudubar da Mai Martaba Sarkin Kano, Lamido Sanusi ya gabatar a Sallar Juma'a a ranar 31 ga watan Mayu ta haifar da cece-kuce a jihar.

Mutane sun yi magana kan hudubar Juma'a da Sanusi II ya gabatar
An zargi Sarkin Kano Sanusi II da yin amfani da mumbari domin yin habaici. Hoto: @masarautarkano
Asali: Twitter

Da yake gabatar da hudubar, Sarki Sanusi II ya ce ba daidai ba ne shugaban musulmi ya ki yarda da duk wata kaddara da ta same shi.

Kara karanta wannan

Kano: Jawabin karshe da Sanusi II ya yi kafin maida shi gadon sarautar Dabo

Hubar Sanusi II ta bar baya da kura

Jama’a da dama a Kano da ma wajen jihar sun yi martani ga hudubar da Sarki Sanusi II ya gabatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani tsohon kwamishinan ayyuka da ababen more rayuwa na jihar Kano, Muaz Magaji, ya zargi Sanusi II da yin amfani da mumbari wajen yin habaici.

"Sanusi II ya koma habaici" - Muaz Magaji

Mista Magaji, wanda ya yi aiki a gwamnatin Ganduje, ya ce hudubar ta yi hannun riga da koyarwar addinin Musulunci kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Facebook.

A cewar Magaji:

"Asalin matsalar shine siyasantar da sarauta da SLS ya yi. Yanzu kuma za a koyawa malamai siyasantar da addini ta hanyar amfani da nassi ana jefa maganganun habaici ga juna."

A wata wallafa da ya yi daban, Magaji ya ce:

Kara karanta wannan

Bidiyon dubban mutane da suka tari Sarkin Kano bayan Juma'a, ya aika sako a huduba

"Mumbari amanar Allah ne! Habaici da nassi a kan mumbari haramun ne! Kuma duk maiyi, mayaudari ne."

"Sanusi II na tallata manufarsa" - Muhammed

Wani ma’abocin Facebook, Adam Muhammed, ya gargadi Sarki Sanusi II kan yin amfani da mumbari wajen tallata manufarsa, in ji rahoton jaridar Leadership.

Ya ruwaito Hadisin wani sahabi, Abu Hurairah wajen kafa hujja kan tuhumar Sanusi II da yi.

“Hadisi na 252, Ibnu Maja ya ruwaito daga Abu Hurairah cewa Annabi Muhammad ya ce: “Duk wanda ya koyi ilmin da ake nema domin Allah, amma ya koye shi domin ya samu wani abin duniya, to ba zai ji kamshin Aljanna ba a ranar kiyama."

Adam Muhammed ya ce laifi ne ga duk wanda ke amfani da wani dandali na yada ilimi, kamar hudubar Juma’a, domin amfanin kansa ko kuma tallata manufarsa.

"Ba mai ja da hukuncinAllah" - Sanusi II

Tun da fari, mun ruwaito cewa, Sarki Muhammadu Sanusi II ya jagoranci sallar Jumu'a a babban masallacin Kofar Kudu a Kano kuma ya yi huɗuba kan imani da Allah.

Sarkin ya bayyana cewa babu wanda zai ja da hukuncin Allah, inda ya ƙara da cewa komai ka ga ɗan adam ya samu ko ya rasa daga Allah ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.