Tsohon sarkin Kano Sanusi II na hudubar Sallar Juma'a a garin Awe

Tsohon sarkin Kano Sanusi II na hudubar Sallar Juma'a a garin Awe

- Tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II na gabatar da hudubar Sallar Juma'a a garin Awe da ke jihar Nasarawa inda a nan ne aka ajiye shi bayan tsige shi daga sarauta

- Sanusi ya yi magana a kan imani da kaddara da kuma hikimomin Ubangiji wajen shirya abubuwa

- Ya ce Duk abin da Allah Ya kaddara wa mutum to lallai akwai alkhairi a cikinsa

Korarren Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II na gabatar da hudubar Sallar Juma'a a garin Awe da ke jihar Nasarawa inda a nan ne aka ajiye shi bayan gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta tsige shi daga sarautar Kano.

A hudubar da yake yi, Sanusi ya yi magana a kan imani da kaddara da kuma hikimomin Ubangiji wajen shirya abubuwa.

Tsohon sarkin Kano Sanusi II na hudubar Sallar Juma'a a garin Awe
Tsohon sarkin Kano Sanusi II na hudubar Sallar Juma'a a garin Awe
Asali: Twitter

Sarkin ya janyo ayoyi da hadisai da suke nuna muhimmancin yarda da kaddara.

"Duk abin da Allah Ya kaddara wa mutum to lallai akwai alkhairi a cikinsa."

KU KARANTA KUMA: Yanzun nan: An tsaurara matakan tsaro a Awe yayinda Sanusi ke shirin bayyana a cikin jama’a don sallar Juma’a

A baya mun kawo maku cewa an fara shirye-shirye domin tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya yi limancin sallar Juma'a a garin Awe.

Wata majiya kwaƙwara ta shaidawa Daily Trust cewa an shirye-shirye domin bawa Sanusi limancin sallar Juma'a duk sati a garin. Masallacin Juma'ar tana hade ne da fadar Sarkin Awe, Alhaji Isa Abubakar Umar.

Matasa sun fara tururuwa zuwa masallacin dauke da taburma da dadduma domin hallartar sallar ta Juma'a.

Idan ba manta ba tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II shine ya ke limancin sallar Juma'a a Kano kafin a lokacin da ya ke sarauta.

Har ila yau mun ji cewa Muhammadu Sanusi na II ya samu yanci inda zai garzaya jahar Lagas.

Bayan Juma'a ne tsohon sarkin da Gwamnan jahar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai Za su tafi Abuja, inda daga nan zai kama hanyar zuwa jahar Lagas.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng