Daliban Jami'a Sun Barke da Murna Yayin da Gwamna Ya Rage 50% Na Kudin Makaranta

Daliban Jami'a Sun Barke da Murna Yayin da Gwamna Ya Rage 50% Na Kudin Makaranta

  • Gwamna Mohammed Umar Bago na Niger ya tallafawa dalibai da ke karatu a Jami'ar Abdulkadir Kure da ke jihar
  • Gwamnan ya rage kudin makaranta da 50% domin rage musu da iyayensu radadin da ake ciki a yanzu a kasar
  • Shugaban Jami'ar, Farfesa Muhammed Yahaya-Kuta shi ya tabbatar da haka a ranar Juma'a 31 ga watan Mayu a birnin Minna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Niger - Gwamnatin jihar Niger ta rage kudin makarantar daliban Jami'a da ke karatu a jihar yayin da ake cikin wani hali.

Gwamnatin ta dauki wannan mataki ne domin ragewa daliban da iyayensu radadin cire tallafin mai.

Gwamna ya rage kudin makarantar dalibai da 50% a Niger
Gwamna Umar Bago ya zaftare kudin rijistar dalibai da 50% a Niger. Hoto: Mohammed Umar Bago.
Asali: Facebook

Niger: Gwamna Bago ya rage kudin makaranta

Kara karanta wannan

Tumatur ya yi tsada a Najeriya, manoma sun fadi abin da ya sa jar miya ta gagara

Matakin ya shafi daliban da ke karatu a Jami'ar Abdulkadir Kure inda aka rage kudin makarantar da 50%, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban Jami'ar, Farfesa Muhammed Yahaya-Kuta ya fitar.

Farfesan ya ce Gwamna Umar Bago ya dauki matakin ne domin saukakawa dalibai da kuma iyayen yara, ThisDay ta tattaro.

Musabbabin rage kudin makarantar ga dalibai

"Gwamna Mohammed Bago ya ce an rage kudin makarantar daliban ne domin rage musu da iyayensu halin matsi da ake ciki."
"Dukkan dalibai da ke karatu a wannan Jami'a sun samu ragin kaso 50 na kudin rijista da za a yi a wannan zango na 2023/2024."

- Muhammed Yahaya-Kuta

Bago ya ce tallafin zai ragewa iyayen da ƴaƴansu matsin da ake ciki dalilin cire tallafin mai a ƙasar.

Kara karanta wannan

Majalisa ta ɗauki mataki kan korar daraktoci da manyan ma'aikata a bankin CBN

Gwamna Nwifuru ya rage kudin makarantar dalibai

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Francis Nwifuru na jihar Ebonyi ya rage kudin karatun jami'ar jihar da kashi 10 cikin 100 domin rage tsadar kudin makarantar.

Gwamnan ya kuma amince da ƙarin albashi na kaso 20% ga malamai da kaso 10% ga ma'aikatan jami'ar jihar Ebonyi.

Nwifuru ya sanar da haka ne a wurin taron yaye talibai karo na 12 zuwa 15 da aka haɗa lokaci guda ranar Asabar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.