Kano: Ƴan Tauri Sun Koka a Fadar Sanusi II Yayin da Gwamnatin Tarayya Ke Gadin Aminu Ado
- Jami'an tsaro sun ja daga a fadar Aminu Ado Bayero yayin da ƴan tauri suka yiwa fadar Muhammadu Sanusi II kuri a Kano
- Mafi yawan jami'an tsaron da ke gadin Aminu Ado daga Gwamnatin Tarayya suke yayin da ƴan tauri suka mamaye fadar Sarki Sanusi II
- Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da dambarwa kan kujerar sarautar jihar fiye da mako guda kenan a Kano
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Yayin da ake ci gaba da dambarwar sarautar Kano, jami'an tsaro sun ci gaba da gadin sarakunan guda biyu.
Yayin da ƴan tauri suka mamaye fadar Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, jami'ai daga Gwamnatin Tarayya ne ke gadin Aminu Ado Bayero.
Jami'an tsaro suna ci gaba da tsaro
An jibge jami'an tsaron ne domin ba da kariya ga Sarkin Kano na 15, Aminu Ado bayan barazanar cafke shi da Abba Kabir ya yi, Premium Times ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A can fadar da Sanusi II ya ke, mafarauta ne da ƴan tauri suka cika fadar domin ba da kariya yayin da suke korafi kan wasu al'amura.
Ƴan taurin suna korafin yadda ba su samun kulawa daga jama'a inda suka yi tsammani ƴan NNPP da dama za su jona layinsu.
Ƴan tauri suna korafi a fadar Sanusi II
Wata majiya ta jiyo suna korafin yadda jama'ar gari ba su nuna musu goyon baya kan yadda suka sadaukar da ransu a fadar.
Har ila yau, sun yi korafi kan wani shugaban riko na karamar hukuma game da rashin sakin kudin abinci har sai da suka yi bore kan lamarin.
Duk wannan abin na faruwa ne bayan zaman dar-dar da ake yi kan kasancewar sarakuna biyu a jhar.
Hakimai sun ziyarci Sanusi II
A wani labarin, kun ji cewa hakimai da dagatai daga ƙauyuka da dama sun kai ziyarar nuna goyon bayan ga Muhammadu Sanusi II a fadarsa.
Bayan hakiman, shugabannin riko na kananan hukumomi 44 da ke jihar ne suka nuna mubaya'a ga sabon Sarkin Kano.
Wannan na zuwa ne bayan wasu daga cikin hakimai suka rasa layin sda za su kama yayin da ake tsaka da rikicin sarautar jihar.
Asali: Legit.ng