Abubuwan Kunya 6 da Suka Faru da Gwamnatin Tinubu a Cikin Shekara 1

Abubuwan Kunya 6 da Suka Faru da Gwamnatin Tinubu a Cikin Shekara 1

Abuja - Daga lokacin da Bola Ahmed Tinubu ya zama shugaban Najeriya, an yi ta samun abin kunya da suka faru da Najeriya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Legit ta fara bibiyar abubuwan da suka auku tun daga Mayun 2023 zuwa yanzu, ta tattaro maku wadanda za a so a manta da su.

Tinubu
Shugaba Bola Tinubu yana ganin kalubale a mulkin Najeriya Hoto: @OfficialABAT
Asali: Twitter

Mulkin Tinubu: Abubuwan kunya da suka faru

1. Juyin mulkin Nijar

Bayan sojoji sun hambarar da gwamnatin Mohammed Bazoum, shugaba Bola Tinubu ya yi kokarin daukar mataki a kan kasar Nijar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lamarin ya kai har shugaban na ECOWAS ya ba kasar Nijar wa’adin maidawa farar hula mulki, amma a karshe sojoji suka kunyata shi.

Kara karanta wannan

Tinubu ya burma matsala, lauyoyi za su maka shi a kotu kan wani kuskuren da ya tafka

Bayan watanni sai ga shi ECOWAS ta janye takunkumin da ta kakaba bayan kuwa tuni kungiyar ta rasa kasashen da ke hannu sojoji.

2. Kamfanin jirgin Emirates

A farkon watan Satumba ne fadar shugaban kasa ta ce jirgin Emirates zai cigaba da tashi bayan ya dakatar da aiki a Najeriya a baya.

Duk da Bola Tinubu ya hadu da Mohamed bin Zayed Al Nahyan, kasar UAE ba ta gaskata labarin ba, wannan abin ya kunyata Najeriya.

3. Fito da takardun sirri

Wani abin kunya da ya rika faruwa a gwamnatin nan shi ne yadda ake fitar da takardun bayanan sirri daga manyan ofisoshi.

Hakan ta faru a wata wasika da George Akume ya rubuta game da N1bn da ake nema domin zaman kwamitin karin albashi.

A irin haka ne kuma aka rika samun bayanai game da kudin da ministar jin-kai, Betta Edu ta batar daga asusun yaki da COVID-19.

Kara karanta wannan

Taken Najeriya: Tinubu ya yi karin haske kan hikimar komawa tsohon taken kasa

4. MAERSK ya kunyata Tinubu

Bayo Onanuga ya fito ya sanar da duniya cewa kamfanin Maersk da ke nahiyar Turai ya yarda zai narka har $600m a Najeriya.

Ba a je ko ina ba sai aka ji kamfanin yana nuna duk da Tinubu ya hadu da Robert Maersk Uggla, bai san da maganar ba tukuna.

5. Jawabi a majalisa

A karshen watan Mayu, Bayo Onanuga ya ce Bola Tinubu zai yi jawabi a gaban ‘yan majalisar wakilai da na majalisar dattawa.

Daga baya sai ga abokin aikinsa, Ajuri Ngalale ya karyata shi, yana mai cewa ba a yanke cewa Tinubu zai yi magana a majalisar ba.

5. Tinubu yana nada mukami, ya sauke

Shugaban kasa ya saba yin nadin mukami sai kuma daga baya a ji ya warware, hakan ya faru tun daga Maryam Shetty a Satumba.

Kwanan nan aka ji Bola Tinubu ya soke nadin Chukwuemeka Woke saboda surutun jama’a, haka aka yi wajen nadin manyan makarantu.

Kara karanta wannan

Ana cikin rigimar sarautar Kano, Ganduje ya sake roƙon ƴan Najeriya

6. Kwan gaba-kwan bayan Tinubu

Alal misali gwamnatin Bola Tinubu ta yi niyyar kawo wasu haraji da hanyoyin tatsar kudi a bankuna, sai kuma aka ji ta watsar da shirin.

An yi ta samun irin wannan a je-a dawo wajen kafa hukumar NELFUND a Najeriya.

Ministocin da Tinubu zai kora

Rahoto ya zo cewa shugaban kasar Najeriya, Bola Tinubu ya fada kuma ya nanata cewa zai kori wasu ministocinsa da ba za su aiki.

An rika jin ra’ayin jama’a a dandalin X game da batun kuma wadanda ake ganin ba su tabuka komai ba sun hada da Adebayo Adelabu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel