Masu Aikin Gina Titun a Najeriya Sun yi Barazana ga Gwamnati, Za su Ajiye Kayan Aiki
- Ma'aikatan kasar nan da ke aikin gina manyan tituna sun yi barazanar tsunduma yajin aiki matukar gwamnatin tarayya ba ta waiwayesu tare da magance matsalolinsu ba
- Ma'aikatan karkashin kungiyoyin manyan ma'aikatan gine-gine ta (CCESSA) da ta kwararrun injiniyoyin aikin kafinta (NUCECFWW) sun fusata da yadda ake korarsu
- Shugabannin kungiyoyin Injiniya Ayodeji Adeyemo da Kwamred Stephen Okoro sun ce an kori ma'aikatansu kimanin 3000 a cikin watanni uku
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Abuja- Kungiyoyin ma'aikatan dake aikin gina titunan kasar nan sun fusata biyo bayan rashin jituwa tsakaninsu da gwamnatin tarayya har ya yi sanadiyyar korar mambobinsu 52,000.
Ma'aikatan da ke aiki a manyan titunan kasar nan sun yi barazanar ajiye kayan aiki su kuma tsunduma yajin aiki nan da kwanaki 21.
Masu aikin tituna za su tafi yaji
Daily Trust ta wallafa cewa idan ba a cimma matsaya ba har suka tafi yajin aiki, titunan da aikinsu zai samu tsaiko suna da yawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daga cikin titunan akwai na Abuja-Kano, Zaria-Sokoto, Lagos-Ibadan, titin Obajana, Kogi-Auchi, Bodo-Bonny da titin Gabas-Yamma.
An kori ma'aikata 3000 a wata 3
Ma’aikatan karkashin kungiyar manyan ma'aikatan gine-gine ta (CCESSA) da ta kwararrun injiniyoyin aikin kafinta (NUCECFWW) sun fusata kan dambarwar dake tsakanin gwamnatin tarayya da masu kwangila.
Kungiyoyin sun zargi sabon ministan ayyuka da kokarin kakabawa ‘yan kwangilar wasu ka’idoji da hukumar sayen kayan jama’a ta BPP ta ba ta amince da su ba.
Injiniya Ayodeji Adeyemo da kwamred Stephen Okoro sun ce dambarwar na kawo tsaikon aiki tare da korar wasu daga ma’aikatansu.
Ana korar ma'aikatan tituna daga aiki
Shugabannin sun kara da cewa an kori ma’aikata akalla 3000 a watanni uku da suka shude, kuma ana sa ran wanna zai sake shafar ma’aikata 32, 000.
A watan Janairun shekarar nan ma sai da suka yi barazanar tsunduma yajin aikin kwanaki uku domin tilastwa gwamnati biyan hakkokinsu kamar yadda Peoples Gazette ta wallafa.
Jirgin kasa: Za a fara jigila a Lagos-Kano
A baya mun ruwaito muku labarin cewa gwamnati na shirye shiryen kaddamar da aikin layin dogo daga Lagos zuwa Kano da zummar fara jigila a watan Yuni.
Ministan sufuri Sa'idu Alkali ne ya bayyana haka lokacin da ya kawo ziyarar aiki jihar Kano domin ganin yadda aikin da aka hada da tashar tsandauri ke wakana.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng