ISWAP Ta Ba Mazauna Garin Kukawa Zabin Barin Gidajensu ko a Kashe Su

ISWAP Ta Ba Mazauna Garin Kukawa Zabin Barin Gidajensu ko a Kashe Su

  • Mazauna Tunbun Rogo a karamar hukumar Kukawa dake jihar Borno sun shiga tsaka mai wuya bayan 'yan ta'addan ISWAP sun umarce su da barin garin daga nan zuwa ranar Asabar
  • Gargadin ya biyo bayan kashe masunta kimanin 35 a daren Lahadi inda yan ta'addar suka zargi mutanen garin da bayar da bayanai a kansu wanda suke yiwa kallon cin amana
  • Rahotanni a baya sun bayyana cewa dama 'yan kungiyar ta ISWAP na zama da mutanen gari kowa na harkokin gabansa, kafin kwatsam su tara su tare da harbe wasu a cikinsu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Borno - Daruruwan mutane ne suke tururuwar barin garinsu a karamar hukumar Kukawa dake jihar Borno bayan 'yan ta'addan ISWAP sun ba su zabi tsakanin mutuwa ko zama daga nan zuwa Asabar mai zuwa.

Kara karanta wannan

'Yan haramtacciyar kungiyar IPOB sun budewa sojoji wuta, jami'an Najeriya sun mutu

A ranar Lahadi da daddare, 'yan ta'addan ISWAP sun kashe akalla masunta 35 a garin Tunbun Rogo dake karamar hukumar Kukawa a Borno.

Gwamnan Borno
Yan kungiyar ISWAP sun bawa mazauna Kukawa zuwa Asabar su bar garinsu ko su mutu Hoto: Babagana Umara Zulum
Asali: Facebook

Daily Trust ta tattaro cewa 'yan ta'addan sun kuma jikkata wasu mutane 25, yayin da aka nemi wasu 30 aka rasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yan ta'adda sun ce an cin amanarsu

Rahotanni sun bayyana cewa mazauna karamar hukumar Kukawa da 'yan ta'addar suna zaune lafiya babu ruwan kowa da kowa.

Amma kwatsam sai aka wayi gari 'yan ta'addar sun tara su inda suka zarge mutanen garin da bayar da bayanai a kansu, kamar yadda Yerwa Express News ta wallafa.

Sun ce ba za su lamunci wannan cin amana ba, inda a nan ne suka harbe mutane akalla 35 wasu kuma suka ruga daji.

Har yanzu akwai gawarwakin da mazauna garin ba su samu daukowa ba, yayin da aka ba su daga nan zuwa ranar Asabar su bar garin.

Kara karanta wannan

'Daɗi zai biyo baya' Masana sun fadi dalilin goyon bayan tsare tsaren Tinubu

'Yan ta'adda sun kashe sojoji

A baya mun kawo muku labarin cewa 'yan ta'addan haramtacciyar kungiyar IPOB sun budewa wasu jami'an sojojin kasar nan wuta tare da kashe guda hudu a jihar Abia.

'Yan ta'addan sun yi ta'asar ne a ranar 30 ga watan Yuni da suke tilastawa jama'ar yankin kudu maso gabas zaman dirshan a gida a fafutukarsu ta kafa kasar Biafra.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.