Rigimar Masarautar Kano: Babbar Kotun Tarayya Na Sama da Babbar Kotun Jiha?

Rigimar Masarautar Kano: Babbar Kotun Tarayya Na Sama da Babbar Kotun Jiha?

  • Maganar da ake yadawa a shafukan sada zumunta na cewa babbar kotun tarayya ta fi kowace babbar kotun jiha ba gaskiya ba ne
  • Hakan ya biyo bayan umarnin kotuna biyu da ke cin karo da juna kan rigimar masarauta tsakanin Aminu Bayero da Muhammadu Sanusi II
  • Wani lauya wanda ya zanta da jaridar Legit, Wale Adeagbo ya ce doka ba ta fifita babbar kotun tarayya a kan babbar kotun jiha ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Wani babban lauya, Wale Adeagbo ya ce dokar kasa ba ta fifita babbar kotun tarayya a kan babbar kotun jiha ba don haka jita-jitar da ake yadawa a intanet ba gaskiya ba ne.

Kara karanta wannan

Kano: Hakimai na cigaba da yiwa Sanusi II mubaya'a duk da barazanar umarnin Kotu

Lauya ya yi magana kan rigimar masarautar Kano
Kano: Babbar kotun tarayya ba ta sama da kowace babbar kotun jiha. Hoto: @Imranmuhdz
Asali: Twitter

Wani mai suna Sambo Mai Hula a shafin X ya yi wannan ikirarin cewa umarnin da babbar kotun tarayya ta bayar kan rigimar masarautar kano na sama da na babbar kotun jihar.

Sanusi II vs Bayero: Kotuna 2 sun yi hukunci

A farkon makon nan ne manyan kotunan biyu suka bayar da umarni ga ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro a kan hambararren sarki Aminu Ado Bayero da kuma batun dawo da Muhammadu Sanusi II.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai shari’a S. Amobeda na babbar kotun tarayya da ke Kano ya bayar da umarni ga jami'an tsaro da su tabbatar da cewa an fitar da Sanusi II daga fada an mayar da Aminu Bayero.

A daya hannun kuma, Mai shari’a Amina Aliyu ta babbar kotun jihar Kano ta umurci jami'an tsaro da kada su kori Sanusi II daga fada kuma ka da a muzguna mashi.

Kara karanta wannan

Sarautar Kano: Lauya ya feɗe gaskiya, ya nemowa Aminu Ado da Sanusi II mafita

Za a kori Sanusi II daga fadar Kano

Abin da sabo mai hula ya ce:

"Babbar kotun tarayya na sama da kowace babbar kotun jiha
"Ka da a yaudare ka, har yanzu Mai martaba Alhaji Aminu Ado Bayero ne Sarkin Kano.
“Ka da ka jefa kanka a rigima da kowa a kan za a kori Sunusi Lamido Sunusi daga Gidan Rumfa.
"Achraf Sunusi ba zai yi fada da jami'an tsaro ba, haka ma wani na kusa da danginsa ko abokansa, don haka yi wa kanka karatun ta nutsu ka zauna a gida."

Matsayin dokar kasa kan kotunan 2

Saboda girman wannan ikirari, jaridar Legit ta zanta da lauya Adeagbo, domin jin ko ikirarin Sambo Mai Hula ya yi dai dai da kundin tsarin mulki.

Adeagbo ya ce:

"Dukkaninsu suna da iko iri daya ne. Dukansu manyan kotuna ne, kawai daya babbar kotun jiha ce daya kuma babbar kotun tarayya ce. Doka ba ta fifita daya a kan daya ba.

Kara karanta wannan

Wa zai zama Sarkin Kano? Abin da kotuna 2 suka ce game da makomar Sanusi II da Aminu

"Umarnin kotunan biyu na wucin gadi ne wanda ba zai haura kwana 7 ba. Dangane da irin wannan takaddamar, ya kamata bangarorin da abin ya shafa su dakata daga daukar kowane irin mataki, a tunkari abin a kotu."

Za a kama masu zanga-zanga a Kano

A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnan jihar Kano, Abba Yusuf ya ba 'yan sanda umarnin kama duk wanda ya fita zanga-zanga a titunan Kano.

Gwammnan ya ba da umarnin ne kan masu yunkurin yin zanga-zanga saboda an rusa masarautun Kano tare da dawo da Muhammadu Sanusi II kan mulki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.