'Yan Sanda Sun Cafke Wanda Ya Kashe 'Yan NYSC a Zanga Zangar Buhari Ya Fadi Zaben 2011

'Yan Sanda Sun Cafke Wanda Ya Kashe 'Yan NYSC a Zanga Zangar Buhari Ya Fadi Zaben 2011

  • An samu barkewar rikici bayan tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fadi zaben shugaban kasar 2011 a garuruwa da dama
  • A dalilin rikicin, an kashe mutane da yawa, a ciki har da masu hidimar kasa a jihar Bauchi da wata 'yar sanda mai suna Rifkatu Bappa
  • Bayan shekaru 13, rundunar yan sanda ta sanar da kama wanda ake zargi ya jogaranci kisan masu hidimar kasa shida a jihar Bauchi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Bauchi -Rundunar yan sanda a jihar Bauchi ta sanar da kama Kabiru Musa da ake zargi ya jagoranci kisan gilla ga masu hidimar kasa (NYSC) shida a shekarar 2011.

Kara karanta wannan

An kama mutumin da ake zargin yana kai wa 'yan bindiga makamai a Plateau

Ana zargin mutumin ya jagoranci kisar gillan ne bayan sanar da cewa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fadi zaben 2011

Police NG
An kama wanda ake zargi da kashe 'yan NYSC a Bauchi. Hoto: Nigerian Police Force
Asali: Facebook

An kashe masu hidimar kasar da wata 'yar sanda a caji ofis a karamar hukumar Giade a jihar Bauchi, rahoton Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bauchi: Yadda aka kashe 'yan NYSC

Yan sanda sun sanar da cewa a ranar 13 ga watan Afrilun 2011, gungun matasa da ake zargin Kabiru Musa ya jagoranta dauke da makamai suka mamaye ofishin yan sanda da ke Giade.

Matasan sun kona ofishin yan sandar wanda ya yi sanadiyyar mutuwar masu hidimar kasa shida tare da ƴar sanda daya mai suna Rifkatu Bappa.

Masu hidimar kasar sun nemi tsira da rayuwarsu amma matasan sun yi nasarar afka musu tare da kashe su baki daya, rahoton Daily Post.

Kara karanta wannan

Tumatur ya yi tsada a Najeriya, manoma sun fadi abin da ya sa jar miya ta gagara

Sunayen 'yan NYSC da aka kashe a 2011

  1. Nkwazema Anslem, daga jihar Imo
  2. Adewumi Seun Paul daga jihar Ekiti.
  3. Okpokiri Obinna, daga jihar Kogi.
  4. Teidi Olawale Tosin, daga jihar Kogi.
  5. Adewei Elliot daga kiahr Bayelsa.
  6. Ukeoma Ikechukwu Chibuzor daga jihar Imo.

'Yan sanda sun yi binciken shekaru 13

Kwamishinan yan sandan jihar Bauchi, Auwal Musa Mohammed ya ce bayan sama da shekara 10 ana bincike kan kisan sun kama wanda ake zargi ya jagoranci ta'addancin.

Ya kuma tabbatar da cewa a yanzu haka suna shirin mika Kabiru Musa zuwa kotu domin alkali ya bincikesa da yanke masa hukunci.

Za a ba 'yan NYSC tallafi

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta ce tana shirin tallafawa masu hidimar kasa domin taimaka musu wajen dogaro da kai da samarwa matasan ayyukan yi.

Ministar matasa, Dr. Jamila Ibrahim da ta bayyana hakan ta ce za a rabawa matasan da ke hidimar kasa 5000 kudi N10m domin bunkasa sana’arsu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng