Yadda na shawo kan Buhari ya amince da sake tsayawa takara - Tony Momoh
- Tsohon ministan sadarwa, Prince Tony Momoh yace bayan zaben 2011 ya shawarci Buhari ya canja ra'ayinsa na kin sake takarar zabe
- Momoh yace duk da cewa shugaban kasar yace ba zai sake tsayawa takarar ba, yana da ikon ya canja ra'ayinsa ko wane lokaci
- Jigon na jam'iyyar APC ya kuma ce kundin tsarin mulki ta bawa shugaban ikon ya sake tsayawa takarar karo na biyu
Wani jigo a jam'iyyar APC, Prince Tony Momoh, a ranar Talata, yace shine ya shawo kan shugaba Muhammadu Buhari ya sake shawara kan tsayawa takarar zabe bayan rashin nasarar da yayi a 2011, ya kara da cewa babu lokacin da Buhari yace bazaiyi tazarce ba kamar yadda Daily Independent ta ruwaito.
Legit.ng ta gano cewa Ciyaman din tsohohuwar jam'iyyar ta CPC, ya ce idan ma shugaba Muhammadu Buhari ya taba fadin cewa ba zaiyi tazarce ba, yana da ikon canja ra'ayinsa kamar yadda yayi tunda dokar kasa bata haramta masa yin hakan ba.
DUBA WANNAN: Gwamna Ortom ya bawa 'yan gudun hijira shawara yadda zasu kare kansu
Tsohon Ministan ya bayyana hakan ne a wata hira da yayi da yan jarida, yace abinda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fada bayan zaben 2011 cewa yayi ba zai sake fitowa takarar shugabancin kasa ba amma ba tazarce ba.
Kazalika, Momoh yace ko a wannan lokacin ya kwabi shugaba Buhari kan fadin wannan maganar inda yace jam'iyya ce take da ikon daukan irin wannan matakin.
"Buhari bai taba cewa ba zaiyi tazarce ba. Buharin da na sani ba zai taba fadin wannan maganar ba. Abinda yace shine ba zai sake fitowa takarar shugabancin kasa ba bayan daya fadi zaben 2011," inji shi.
A yayin da yake mayar da martani kan wasikar da Olusegun Obasanjo, jigon na jam'iyyar APC yace Obasanjo bashi da damar ya fadawa Buhari abinda zaiyi tunda shi ba dan jam'iyyar APC bane.
"Muna da mutanen da sukayi gwagwarmayar zarcewa kan mulki har karo na uku. Amma don wannan bawan Allah ne neman zarcewa karo na biyu sai gasu sun fito suna cewa kar ya zarce," inji shi.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng