“Karancin Kudi”: Kungiyar ASUU Ta Tsunduma Yajin Aiki a Jami’ar Kano, Ta Bayyana Dalili
- Kungiyar malaman jami'o'i (ASUU) reshen jami'ar Yusuf Maitama Sule da ke jihar Kano ta shiga yajin aikin gargadi na mako biyu
- A cikin wata sanarwa daga shugabannin kungiyar, sun shiga yajin aikin ne saboda karancin kudin da suke samu daga gwamnati
- A cewar kungiyar, gwamnatin jihar ta yi biris da duk wani kokari na ganin an zauna a teburin sasanci domin magance matsalar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano – Kungiyar malaman jami’a (ASUU) a jami’ar Yusuf Maitama Sule ta Kano, ta fara yajin aikin gargadi na tsawon mako biyu.
A baya dai kungiyar ta koka kan rashin kudi da jami'ar ke fama da shi yayin da gwamnatin jihar ta kashe biliyoyin Naira wajen tura dalibai zuwa karatu a jami’o’in kasashen waje.
Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa malaman sun ce jami’ar na dab da shiga fatara bayan shekaru ta na fama da karancin kudi daga gwamnatin jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
ASUU ta fara yajin aiki a Kano
A wata sanarwa dauke da sa hannun shugaba da kuma sakataren kungiyar ASUU, Mansur Sa’id da Yusuf Gwarzo, malaman sun ce har yanzu ba a magance koke-koken da suke yi na rashin kudi a jami’ar ba.
Kungiyar ta ce ta cimma matsayar ta na fara yajin aikin ne a taron da ta gudanar a ranar Laraba, 29 ga watan Mayu, in ji rahoton jaridar Independent.
Sanarwar ta kara da cewa:
Kungiyar ta amince da shiga yajin aikin gargadi na makwanni biyu, kuma idan ba a samu wani kwakkwaran alkawari daga gwamnati ba, malaman za su zarce da yajin aikin na dindindin.”
- ASUU, YUMSUK
Abin da ya jawowa ASUU shiga yajin aikin
A watan Nuwamban 2023, ASUU ta yi zargin cewa gwamnatin jihar ta yi watsi da bukatar ta na tattaunawa kan kalubalen da jami’ar ke fuskanta.
A cewar kungiyar, bukatun ta sun mayar da hankali ne kan bangarori uku da suka shafi: inganta yanayin aikin ma'aikata, isassun kudi, da kare 'yancin cin gashin kai da 'yancin karatun jami'ar.
Rigimar masarautar Kano da hukuncin kotu
A baya, Legit Hausa ta ruwaito cewa wasu umarni da kotuna biyu suka bayar kan rigimar masarautar Kano tsakanin Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero sun jawo rudani.
A yayin da babbar kotun tarayya ta bayar da umarnin a fitar da Sanusi II daga gidan sarauta, ita kuma babbar kotun jiha ta yi gargadi kan taba sabon sarkin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng