Sarautar Kano: NNPP ta Tsoma Baki Kan Lamarin, Ta Nemowa Sanusi II da Aminu Ado Mafita

Sarautar Kano: NNPP ta Tsoma Baki Kan Lamarin, Ta Nemowa Sanusi II da Aminu Ado Mafita

  • Yayin da ake ci gaba da dambarwa kan sarautar jihar Kano, jam'iyyar NNPP ta tsoma baki kan rikicin a jihar
  • Jam'iyyar ta bukaci duka bangarorin biyu da ke neman kwace kujerar da su yi taka tsan-tsan wurin bin doka da oda
  • Uban jam'iyyar a Najeriya, Dakta Boniface Aniebonam shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa a jihar Lagos

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Jam'iyyar NNPP ta yi martan kan rikicin sarautar Kano da ya ki ci ya ki cinyewa har zuwa yanzu.

Jam'iyyar NNPP ta bukaci a bi tsarin doka da oda domin warware matsalar sarautar jihar ba tare da matsala ba.

Kara karanta wannan

Majalisa ta ɗauki mataki kan korar daraktoci da manyan ma'aikata a bankin CBN

NNPP ta magantu kan rikicin sarautar Kano, ta nemo mafita
Jami'yyar NNPP ta bukaci bin doka yayin kawo karshen rikicin sarautar Kano. Hoto: Sanusi Lamido Sanusi, Masarautar Kano.
Asali: Facebook

Jigon NNPP ya magantu kan sarautar Kano

Wanda ya assasa jam'iyyar a Najeriya, Dakta Boniface Aniebonam ya bayyana haka a yau Alhamis 30 ga watan Mayu a jihar Lagos, cewar Daily Nigerian.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Aniebonam ya bukaci bin lamarin a hankali domin samar da tsaro cikin jihar ba tare da tayar da hankula da jefa jama'a cikin rudani ba.

Martanin jami'yyar na zuwa ne yayin da ake ci gaba da dambarwa kan rikicin sarautar jihar da ya ki karewa tun a makon jiya.

Kano: NNPP ta nemo mafita kan sarauta

"Jihar Kano ce kawai NNPP ke mulka, a matsayinmu na jam'iyya mai son zaman lafiya, mun yarda da bin doka."
"Ya kamata mu kula da zaman lafiyar jihar Kano fiye da muradun wasu daidaiku."
"Abin da ya fi muhimmanci a kokarin neman kujerar sarautar jihar shi ne duka bangarorin biyu su tabbatar da bin doka da oda."

Kara karanta wannan

Duk da umarnin kotu da ke neman sauke Sanusi II, Mataimakin Gwamna ya gana da Sarki

- Boniface Aniebonam

Gwamnan Kano ya gana da nuna Ribadu

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Abba Kabir ya gana da mai ba Bola Tinubu shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu.

Abba Kabir ya yi ganawar da Malam Ribadu ne a ofishinsa da ke birnin Abuja a yau Alhamis 30 ga watan Mayun 2024.

Wannan ganawa na zuwa ne bayan zargin Ribadu da hannu a rikicin sarautar jihar Kano, daga baya aka janye zargin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.