An Rasa Rayuka Bayan 'Yan Bindiga Sun Farmaki Sojoji a Shingen Bincike

An Rasa Rayuka Bayan 'Yan Bindiga Sun Farmaki Sojoji a Shingen Bincike

  • Wasu miyagun ƴan bindiga sun kai farmaki kan sojojin Bataliya ta 144 da ke garin Aba, cibiyar kasuwancin jihar Abia suna tsaka da gudanar da aikinsu
  • Ana fargabar ƴan bindigan waɗanda suka kai harin cikin wata mota ƙirar SUV sun hallaka sojoji uku a yayin farmakin da suka kai musu
  • Ƴan bindigan sun kuma ƙona motar sintirin sojojin tare da yin awon gaba da bindigan jami'an tsaron bayan sun kai musu farmaki a shingen bincikensu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Abia - Ana fargabar ƴan bindiga sun kashe sojoji uku na rundunar birged 14 ta sojojin Najeriya da ke Ohafia a jihar Abia.

Ƴan bindigan sun hallaka sojojin ne waɗanda ke aiki da bataliya ta 144 a garin Aba, cibiyar kasuwancin jihar Abia.

Kara karanta wannan

"Mun gaji da rikici": Matasa sun ɗauki zafi, sun shiga fada sun taso sarki waje

'Yan bindiga sun farmaki sojoji a Abia
'Yan bindiga sun hallaka sojoji a Abia Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

Sojoji sun gamu da sharrin 'yan bindiga

An kashe sojojin ne a wajen shingen binciken sojojin da ke kan kwanar Obikabia kusa da Umuola a ƙaramar hukumar Aba ta Arewa, cewar rahoton jaridar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan bindigan da suka rufe fuskokinsu, sun zo ne cikin wata mota baƙa ƙirar SUV wanda ya nuna sun batar da kamanni.

Miyagun sun shammaci sojojin da suke bakin aiki lokacin da suka kai musu harin.

An tattaro cewa ƴan bindigan sun kuma yi awon gaba da bindigun sojojin wanda hakan zai ba su damar yin wata ta'asar.

'Yan bindigan ba su tsaya nan ba, sun kuma ƙona motar sintirin da jami’an tsaron ke amfani da ita da shingen binciken kafin su tafi.

Ƴan bindiga sun kashe sojoji

A baya Legit Hausa ta kawo labarin cewa rundunar sojojin Najeriya ta tabbatar da kisan wasu jami’anta da ke aiki da ‘operation hadarin daji’ guda huɗu a jihar Katsina.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun kai farmaki cikin kasuwa a Kaduna, an rasa rayukan bayin Allah

Rahotanni sun bayyana cewa wasu ƴan ta’adda sun kai hari sansanin sojoji a karamar hukumar faskari da ke jihar Katsina ranar Lahadi.

Direba ya hallaka soja a Legas

A wani labarin kuma, kun ji cewa direban wata babbar motar wani kamfanin hada-hadar kayayyaki ta murƙushe wani soja har lahira a madakatar mota ta Orile da ke Iganmu a jihar Legas.

Direban babbar motar ya bi ta kan sojan ne a ƙoƙarinsa na tserewa wasu matasa da ke karɓar kuɗi daga hannun direbobin motocin haya a Orile, ƙarshen babban titin Badagry.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng