"Mun Gaji da Rikici": Matasa Sun Ɗauki Zafi, Sun Shiga Fada Sun Taso Sarki Waje

"Mun Gaji da Rikici": Matasa Sun Ɗauki Zafi, Sun Shiga Fada Sun Taso Sarki Waje

  • Wasu gungun matasa sun shiga fadar sarkin masarautar Okuku a ƙaramar hukumar Yala ta jihar Kuros Riba, sun watso shi waje
  • Rahotanni sun nuna matasan sun ɗauki wannan matakin ne bayan basaraken ya gaza kiran taron sulhu kan rikicin da ke faruwa a garinsa
  • Rundunar ƴan sandan jihar Kuros Riba ta ce a halin yanzu jami'anta na kan bincike kan lamarin wanda ya auku jiya Laraba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Cross River - Wasu fusatattun matasa sun kutsa kai har cikin fadar sarkin Okuku, HRH Chief Odaji Ipuole, sun fito da shi waje a ƙaramar hukumar Yala da ke jihar Kuros Riba.

Matasan da suka zo wuya kan halayen sarkin, sun ɗauki wannan matakin ne saboda ya ƙi sasanta rikicin da ya ɓarke a yankinsa.

Kara karanta wannan

Sojoji sun ragargaji 'yan ta'adda a jihar Kaduna, sun cafke masu ba su bayanai

Sufetan yan sanda, IGP Kayode.
Matasa sun ɗauki zafi, sun fatattaki sarki daga fadarsa a Cross River Hoto: PoliceNG
Asali: Facebook

Daily Trust ta tattaro cewa lamarin ya faru ne jiya Laraba lokacin da matasan suka fara zargin basaraken ya kasa kiran taro domin kawo ƙarshen rikicin da ke faruwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rikicin da yake faruwa a Okuku

Yankin masarautar Okuku a ƙaramar hukumar Yala na fama da rigingimun ƙabilanci da sauran matsaloli da suka hana al'umma zaman lafiya.

Sakamakon haka ne matasan ke ganin sarkin ba shi da halaye masu kyau saboda tsame hannunsa daga abubuwan da ke faruwa ya ƙara dagula lamarin.

Matasan sun gudanar da zanga-zangar lumana har zuwa fadar basaraken suna rera wakoki, daga bisani suka kore shi dga fadar.

A cewarsu, fadar za ta ci gaba da kasancewa a rufe har sai basaraken ya shirya magance matsalolin da suka shafi al’ummar da yake jagoranta.

Matasa sun ɗauki mataki kan sarki

Kara karanta wannan

Kotu ta kori ƴan APC 25, ta hana su ayyana kansu a matsayin 'yan majalisa

Wani magidanci mai suna Pius Ireti ya ce gabanin a kawo wannan matakin, matasan sun roki sarkin ya gayyaci bangarorin zuwa taron zaman lafiya amma ya ƙi.

Ya ce:

"Saboda kin kira taron, matasa suka rubuta wasiƙa zuwa majalisar sarakunan Yala ta Gabas, suka nemi kar a kara barin wani basarake daga Okuku da Ogbaniko ya halarci taron sarakuna."

Jami’ar hulda da jama’a ta rundunar ‘yan sandan jihar, Irene Ugbo, ta ce rundunar tana gudanar da bincike kan lamarin.

Ƴan kwadago sun rage buri

A wani rahoton kuma ƴan kwadago sun bayyana cewa za su rage adadin kuɗin da suke buƙatar a biya a matsayin mafi ƙarancin albashi a Najeriya.

Shugaban TUC, Festus Osifo, ya ce gwamnatin tarayya ba da gaske take ba da ta gabatar da tayin N60,000 a taron ranar Talata.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel