Direban Motar Kamfani Ya Murkushe Sojan Najeriya Har Lahira a Legas

Direban Motar Kamfani Ya Murkushe Sojan Najeriya Har Lahira a Legas

  • Wani mummunan ifitila'i ya afku a madakatar mota ta Orile da ke Iganmu a Legas, inda direban mota ya kashe wani soja bayan ya bi ta kansa
  • Wani da abin ya faru a kan idanunsa ya bayyana cewa sojan na kan babur dinsa lokacin da motar ta murkushe shi, inda nan take ya mutu
  • Amma an ce wasu sojoji da lamarin ya faru a kan idon su sun bi bayan babbar motar a lokacin da direban ya yi niyyar tserewa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Legas - A ranar Talatar ne wata babbar motar wani kamfanin hada-hadar kayayyaki ta murkushe wani soja har lahira a madakatar mota ta Orile da ke Iganmu a Legas.

Kara karanta wannan

Hallaccin 'Mining': Abin da malamin musulunci ya ce game da Notcoin da TapSwap

Mota ta murkushe soja har lahira a Legas
Direba ya bi ta kan wani soja a Legas, ya mutu nan take. Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Facebook

Sojoji sun kamo diren motar

An ce direban babbar motar ya bi ta kan sojan ne a kokarinsa na tserewa wasu matasa da ke karbar kudi daga hannun direbobin motocin haya a Orile, karshen babban titin Badagry.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar Daily Trust ta ruwaito direban ya yi biris da abin da ya faru inda ya kwashi motar a guje da nufin tserewa daga wajen.

An ce wasu sojoji da lamarin ya faru a kan idon su sun bi bayan babbar motar a guje domin kama direban.

An tattaro cewa daga karshe sojojin sun kama motar a tashar motar Mile 2, amma kwandastan motar ya yi nasarar tserewa.

Motar ta murkushe sojan a kan babur

Shola James, wani dan kasuwa a Orile, ya bayyana cewa sojojin sun tasa keyar direban da motar zuwa Orile.

Kara karanta wannan

Ba a manta da kisan Ummita a Kano ba, wani ɗan China ya sake kashe ‘yar Najeriya

Wani ganau mai da ke aikin faci, ya yi ikirarin cewa sojan na kan babur dinsa lokacin da motar ta bi ta kanshi, a nan take ya mutu.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Legas, Benjamin Hundeyin, ya bayyana cewa ba a kai direban ga ‘yan sanda ba.

Abia: Dan China ya kashe 'yar Najeriya

A wani labarin, mun ruwaito cewa ana zargin wani dan China ya kashe wata matashiya a jihar Abia saboda ta ki yarda su yi soyayya.

An ce dan birnin Sin din na aiki a matsayin shugaban matashiyar mai suna a wani kamfanin karafa da ke jihar, kuma ya tunkudo ta daga saman babbar mota.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel