Sarautar Kano: Lauya Ya Feɗe Gaskiya, Ya Nemowa Aminu Ado da Sanusi II Mafita

Sarautar Kano: Lauya Ya Feɗe Gaskiya, Ya Nemowa Aminu Ado da Sanusi II Mafita

  • Fitaccen lauya a Najeriya, Wale Adeagbo ta magantu kan umarnin kotuna masu cin karo da juna a rikicin sarautar jihar Kano
  • Barista Adeagbo ya ce duka kotunan sun ba da umarnin ne bisa ikonsu kuma babu inda Babbar Kotun Tarayya ta fi ta jiha
  • Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da zaman dar-dar a Kano bayan tuge Aminu Ado Bayero tare da mayar da Sanusi II

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Yayin da ake samun sabani kan umarnin kotuna game da masarautun jihar Kano, fitaccen lauya ya yi karin haske.

Wale Adeagbo ya ce babu inda a cikin kundin tsarin mulkin Najeriya aka ce Babbar Kotun Tarayya ya fi babbar kotun jiha iko.

Kara karanta wannan

Wa zai zama Sarkin Kano? Abin da kotuna 2 suka ce game da makomar Sanusi II da Aminu

Lauya ya magantu kan rikicin sarautar Kano tsakanin Aminu Ado da Sanusi II
Lauya Wale Adeagbo ya fayyace matsalar umarnin kotuna game da masarautun jihar. Hoto: Masaraurar Kano, Sanusi Lamido Sanusi.
Asali: Facebook

Kano: Lauya ya magantu kan rikicin sarauta

Adeagbo ya bayyana haka yayin hira da jaridar Legit inda ya ce duka kotunan sun yi hukuncin ne bisa ikonsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lauyan ya ce babu inda aka fifita daya a kan daya sai dai kawai bambancinsu shi ne daya daga jiha take daya kuma daga Gwamnatin Tarayya.

"Wannan umarnin kotuna kawai an bayar da shi ne ga bangare daya wanda ba zai dauki lokaci ba."
"Mafi yawanci irin wannan umarni na kotu ba ya wuce mako daya."
"Game da wannan umarnin kotuna masu karo da juna da aka bayar, ya kamata wadanda abin ya shafa cikin har da ƴan sanda su kalubalanci umarnin a gaban kotu."

- Wale Adeagbo

Sarautar Kano: Umarnin kotuna masu cin karo

Wannan na zuwa ne yayin da kotuna suka ba da umarni masu cin karo da juna tun farkon fara dambarwar masarautun jihar Kano.

Kara karanta wannan

Kano: An shiga ɗimuwa bayan jin harbe harbe a fadar da Aminu Ado Bayero yake

Tun farko, Babbar Kotun Tarayya ta ba da umarnin dakatar da mayar da Muhammadu Sanusi II kan kujerarsa.

Daga bisani kuma babbar kotun jiha ta umarci a tuge sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero daga fadar Nasarawa.

A jiya Talata 28 ga watan Mayu kuma Babbar Kotun Tarayya ta umarci jami'an tsaro su tuge Muhammadu Sanusi II daga kan karagar mulki.

Ribadu ya yi barazana ga gwamnatin Kano

Kun ji cewa, Mallam Nuhu Ribadu ya yi barazanar maka gwamnatin jihar Kano a kotu kan zarginsa da suka yi a rikicin sarautar jihar.

Ribadu ya musanta hannu a zargin da ake yi masa inda ya bukaci su kawo gamsassun hujjoji sabanin haka kuma zai dauki mataki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.