Taken Najeriya: Tinubu Ya Rattaba Hannu Kan Muhimmin Kudirin da Majalisa Ta Zartar

Taken Najeriya: Tinubu Ya Rattaba Hannu Kan Muhimmin Kudirin da Majalisa Ta Zartar

  • Daga wannan ranar ta 29 ga watan Mayun 2024, Najeriya ta daina amfani da taken kasa na “Ku tashi, ya ku ‘yan kasa”
  • Shugaba Bola Tinubu ya rattaba hannu a kan dokar dawo amfani da tsohuwar wakar taken kasar ta “Nigeria, mun jinjina miki”
  • A shekarar 1978 ne sojoji suka soke amfani da tsohon taken kasar, bayan shekaru 46 kuma Shugaba Bola Tinubu ya dawo da shi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya rattaba hannu a kan kudirin dokar taken Najeriya da majalisar dokokin kasar ta zartar a ranar Talata.

Da wannan kudiri da Bola Tinubu ya amince da shi a yau Laraba, za a dawo amfani da tsohuwar wakar taken kasar ta “Nigeria, mun jinjina miki”.

Kara karanta wannan

Wa zai zama Sarkin Kano? Abin da kotuna 2 suka ce game da makomar Sanusi II da Aminu

Tinubu ya rattaba hannu kan dokar taken Najeriya
Tinubu ya sa hannu kan dokar komawa amfani da tsohon taken Najeriya. Hoto: @HouseNGR
Asali: Twitter

A shekarar 1978 ne sojoji suka soke amfani da tsohon taken kasar, bayan shekaru 46 kuma Shugaba Bola Tinubu ya rattaba hannu kan dokar dawo da taken, in ji rahoton Arise TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya amince da tsohon taken Najeriya

Shugaban majalisar dattijai, Godswill Akpabio, a wani zama na hadin guiwa na majalisar tarayya ya ce Bola Tinubu ya rattabu hannu kan kudurin dokar kuma zai kaddamar da taken.

Channels TV ta ruwaito Tinubu ya tabbatar da komawa amfani da taken ‘'Nigeria, mun jinjina miki'’ maimakon taken “Ku tashi, ya ku ‘yan kasa” a zaman taron hadin gwiwa na majalisar.

A baya mun ruwaito majalisar dattawa da ta wakilai sun amince da dokar sauya taken kasar daga a wasu zaman majalisar daban-daban.

Yadda ake rera sabon taken Najeriya

Tsohon hadimin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ta fuskar kafofin sada zumunta, Bashir Ahmad ya wallafa taken da za a rika amfani da shi yanzu a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da cin kwakwa, Majalisa ta sauya taken Najeriya, ta fadi amfaninsa

Saurari yadda ake rara taken a nan kasa:

"Hanyoyin farfado da tattalin Najeriya" - Atiku

A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya soki manufofin gwamnatin Bola Tinubu, yana mai zargin an kara talauta 'yan kasar.

Jigon 'yan adawar, ya ba Tinubu shawarar hanyoyin da zai bi domin dawo da martabar Najeriya da kuma farfado da tattalin arzikin kasar da ma gyara matsalar tsaro.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel