Hajjin 2024: Allah Ya Yiwa Wani Alhaji Daga Najeriya Rasuwa a Makkah
- Allah ya yiwa ɗaya daga cikin alhazan Najeriya daga jihar Legas, Idris Oloshogbo rasuwa a Makkah bayan ya dawo daga ɗawafi
- Babban sakataren hukumar jin daɗin alhazai na jihar, Saheed Onipede ne ya tabbatar da haka a wata sanarwa ranar Laraba
- Ya ce tuni aka yiwa marigayin janaza bisa dokokin da hukumomin Saudiyya suka shinfida, kana ya roƙi Allah ya gafarta masa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Rahotanni sun nuna cewa ɗaya daga cikin alhazan jihar Legas mai suna, Idris Oloshogbo, ɗan kimanin shekaru 68 a duniya ya rasu a ƙasa mai tsarki.
Likitocin ƙasar Saudiyya ne suka tabbatar da rasuwar Alhaji Oloshogbo a birnin Makkah.
Makkah: Mai shirin zama Alhaji ya rasu
Jaridar Vanguard ta tattaro cewa Oloshogbo ya rasu ne jim kadan bayan ya dawo daga ɗawafin Ka’aba a Makkah.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sakataren hukumar jin dadin alhazai ta jihar Legas, Saheed Onipede, ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa ta hannun mai magana da yawun hukumar, Taofeek Lawal a ranar Laraba.
A cewar Onipede, marigayin wanda ya fito daga karamar hukumar Shomolu a jihar Legas ya rasu ne a lokacin da yake cin abincinsa da yamma bayan Sallar Magriba.
Duk da har yanzu likitoci ba su bayyana asalin abin da ya zama ajalinsa ba, Onipede ya ce lamarin ba zai rasa alaƙa da hawan jini ba tare da lura da yadda ya jigata.
Gwamnatin Legas ta yi ta'aziyya
Ya kuma miƙa sakon ta'aziyya ga iyalai, ƴan uwa da abokan arzikin mamacin a madadin gwamnatin jihar Legas.
Onipede ya roki Allah ya gafarta masa kura-kuransa, ya kuma ba shi Aljannar Firdausi da ladan aikin Hajji, tunda ya riga ya yi niyya, rahoton Tribune Nigeria.
Don haka ya yi kira ga sauran alhazai da su yi taka-tsan-tsan tare da kiyaye cikawa kansu aiki tun kafin a fara aikin Hajji na hakika wanda ya zama wajibi.
An yiwa mamacin jana'iza a Makkah
"An yi jana'izar marigayin a Makkah bisa ka'idojin da hukumomin Saudiyya suka shimfida," in ji Onipede.
Wani ma’aikacin hukumar, Waheed Shonibare ne ya jagoranci wasu jami’an gwamnatin jihar da wasu mahajjata wajen gudanar da sallar janaza ga mamacin a masallacin Ka'abah.
An biyawa yaro kuɗin hajji
A wani rahoton kuma an ji cewa an karrama yaron da ya nuna hadda da sanin ma'anonin Alkur'ani a jihar Kano da kujerar zuwa aikin Hajji.
Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano ce ta bayyana kyautar tare da fadi dalilai da suka sa aka karrama mahaddacin da damar sauke farali.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng