Jerin Alkawuran da Shugaba Bola Tinubu Ya Gagara Cikawa Cikin Shakara 1

Jerin Alkawuran da Shugaba Bola Tinubu Ya Gagara Cikawa Cikin Shakara 1

  • A yau Laraba, 29 ga watan Mayu shugaban kasa Bola Tinubu ya cika shekara daya da rantsuwar fara shugabancin Najeriya
  • Tun kafin a rantsar da shi, shugaban kasar ya yi alkawura daban-daban a harkokin ilimi, tsaro farfaɗo da tattalin arziki da dai sauransu
  • Bayan shafe shekara daya a kan karaga, Legit ta yi waiwaye domin ganin ko shugaban kasar ya cika alkawuran kamar yadda ya yi su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - A yau Laraba shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya cika shekara daya kan karagar mulkin Najeriya.

Tinubu
Tinubu ya gaza cika manyan alkawura da ya yi bayan shafe shekara kan mulki. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Tun lokacin zabe da ma farkon hawansa mulki, shugaba Tinubu ya yi alkawura da dama ga mutanen Najeriya, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Atiku ya ragargaji Tinubu, ya fadi abin da ya sa aka gaza gyara Najeriya

A wannan rahoton, Legit ta yi nazari kan alkawura daban-daban da shugaban kasar ya yi da lura da ko ya cikasu kamar yadda ya dauka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Tinubu ya ce zai samar da tsaro

Shugaba Bola Tinubu ya yi alkawarin inganta harkar tsaro a fadin Najeriya a lokacin da yake neman zabe.

Amma sai dai a halin da ake ciki lamarin tsaro ya kara tabarbarewa. Yan bindiga sun cigaba da kai hare-hare cikin kauyuka da satar mutane, ko a makon da ya wuce an sace mutane kimanin 80 a jihar Katsina.

2. Inganta wutar lantarki

A cikin jawabin karbar mulki da shugaban kasar ya yi, ya yi alkawarin inganta wuta domin bunkasa sana'o'i.

Sai dai an cigaba da samun matsalolin wuta, tun daga karin kudin lantarki, faduwar turakan wuta da kuma uwa uba lalacewar wuta a yankin Arewa maso gabas.

Kara karanta wannan

Jam’iyyun siyasa sun yi kewar Buhari, ana Allah wadai da shekarar farko a mulkin Tinubu

3. Gwamnatin Tinubu da karin albashi

Tun kafin zabe da kuma kwanaki kadan bayan rantsar da shi, shugaba Tinubu ya fara alkawari da tattaunawa da kungiyar kwadago kan karin albashi.

Amma yau shekara daya cif ba a samu daidaito kan karin albashi ba balle a fara biya. Abin da aka samu kawai shi ne N35,000 ga wasu ma'aikata domin rage radadin cire tallafin man fetur.

Sauran alkawura da ba su samu cika ba sun hada da farfaɗo da darajar Naira, inganta harkar noma.

Ba a daidaita kan karin albashi ba

A wani rahoton, kun ji cewa Gwamnatin tarayya ta sake gamuwa da cikas daga ƴan kwadago bayan ta gabatar da tayin N57,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi.

Rahotanni sun nuna ƴan kwadago a Najeriya sun yi fatali da tayin a karo na uku amma sun rage bukatarsu daga N615, 000 zuwa N497, 000.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng