Wa Zai Zama Sarkin Kano? Abin da Kotuna 2 Suka Ce Game da Makomar Sanusi II da Aminu

Wa Zai Zama Sarkin Kano? Abin da Kotuna 2 Suka Ce Game da Makomar Sanusi II da Aminu

Jihar Kano - Wasu kotuna biyu a jihar Kano sun fitar da wasu umarnin wucin gadi wadanda suka cin karo da juna kan rikicin masarautar Kano.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

A ranar Talata, Mai shari’a S. A. Amobeda na babbar kotun tarayya ya bayar da umarnin korar Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi II daga fadar Gidan Rumfa.

Sai dai Mai shari’a Amina Adamu Aliyu ta babbar kotun jihar Kano ta bayar da wani umarni na daban, inda ta haramtawa jami'an tsaro kora, muzgunawa ko kama Sanusi II.

Rigimar masarautar Kano tsakanin Sanusi II da Aminu
Kotuna 2 sun ba da umarni da ya sabawa juna kan rigimar masarautar Kano. @masarautarkano, @Imranmuhdz
Asali: Facebook

Muhammadu Sanusi II da Aminu Bayero na kan fafatawa a neman kujerar sarautar Kano. Rigimar dai ta janyo zanga-zangar magoya bayansu a sassan jihar.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da ruɗanin hukuncin kotuna 2, jigon NNPP ya yi magana kan naɗin Sarkin Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da kotuna biyu suka ce da ya jawo rudani:

Kotu ta ba da umarnin korar Sanusi II

Mun ruwaito cewa wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano a ranar Talata ta bayar da umarnin korar Sanusi I daga fadar Gidan Rumfa.

Kotun ta kuma umarci ’yan sanda da su tabbatar an ba Sarkin Kano na 15, Aminu Bayero duk wani hakki da alfarma da ya kamata a ba shi.

Mai shari’a S. A. Amobeda wanda ya bayar da wannan umarnin ya bayyana cewa an yi wannan hukunci ne domin tabbatar da adalci da kuma wanzar da zaman lafiya a jihar Kano.

An dage sauraron karar zuwa ranar 4 ga watan Yuni domin a fara sauraren kowanne bangare.

An hana jami’an tsaro korar Sanusi II

Mai shari’a Amina Adamu Aliyu ta babbar kotun Kano da ke zamanta a titin Miller, ta hana ‘yan sanda, hukumar tsaro ta farin kaya, SSS da sojojin Najeriya korar Sanusi II daga fada.

Kara karanta wannan

Kano: Kotu ta umarci a fitar da Muhammadu Sanusi II Daga Fadar Sarki

Sarkin ne ya shigar da karar tare da masu nadin sarkin Kano hudu: Madakin Kano Yusuf Nabahani; Makaman Kano Ibrahim Sarki Abdullahi; Sarkin Bai Mansur Adnan da Sarkin Dawaki Maituta Bello Tuta.

Mun ruwaito cewa Mai shari’a Amina Aliyu ta kuma hana jami’an tsaron kamawa ko musgunawa Sarkin da masu nadin sarki.

An dage karar zuwa ranar 13 ga Yuni, 2024 domin fara sauraren kowanne bangare.

Hakimai 40 sun bi Sarki Sanusi II

A wani labarin, mun ruwaito akalla hakimai 40 ne suka kai caffa ga mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II domin nuna mubayi'arsu ga nadin da aka yi masa a matsayin sarki.

Kano na da hakimai 65, wanda mubayi'ar 40 ga Sarkin Kano Sanusi II na nufin ya samu rinjaye goyon bayan hakiman a kan wadanda suka goyi bayan Aminu Ado Bayero.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel